Iyalaina yanzu sun koma Ilori, Sarkin Fulanin Igangan a jihar Oyo

Iyalaina yanzu sun koma Ilori, Sarkin Fulanin Igangan a jihar Oyo

- Sarkin Fulanin da aka kora tare da iyalansa daga jihar Oyo ya yi gudun Hijra Ilori

- Ya bayyana yadda aka kona masa gida da dukiya a garin Igangan

- Sunday Igboho ya cika da lashe takobin koran Fulani makiyaya daga kasar Yarabawa

Bayan korarsu daga jihar Oyo, Sarkin Fulanin Igangan, Salihu Abdulkadir, ya bayyana cewa yana kan hanyan zuwa Arewa yayinda iyalansa suka yi gudun hijra Ilori, birnin jihar Kwara.

Sarkin Fulanin da iyalansa sun gudu daga Igangan ne ranar Juma'a bayan wa'adin da wani matashin mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Igboho, ya basu na cewa su fita daga kasar saboda garkuwa da mutane da Fulani ke yi.

Abdulkadri ya bayyana cewa yan uwansa dake Ilori suka tarbesa, The Punch ta ruwaito.

Yayinda aka tambayesa kan yadda zai yi sulhu da al'ummar garin Igangan, yace, "Har yanzu ba'a kira ni don wani tattaunawa ba. Idan aka ce mu koma Igangan, ina zamu zauna? An kona min gida da motoci."

"Amma idan aka bani daman komawa, zan yi nazari kan hakan."

"Lokacin da aka koremu daga Igangan, mun koma Ilori a jihar Kwara. Yanzu haka ina Arewa amma yarana na Ilori. Ina da gida a Ilori."

KU KARANTA: Bayan shekaru biyar, an ceto daya daga cikin yan matan Chibok

Iyalaina yanzu sun koma Ilori, Sarkin Fulanin Igangan a jihar Oyo
Iyalaina yanzu sun koma Ilori, Sarkin Fulanin Igangan a jihar Oyo
Asali: UGC

KU KARANTA: Buratai ya mika mulki ga sabon shugaban hafsan sojin kasa, Ibrahim Attahiru (Hotuna)

A bangare guda, mai rajin kare rayukan Yarabawa, Sunday Adeyemo Igboho, ya bayyana cewa bayan samun nasaran fitittikan Fulani daga jihar Oyo, yanzu jihar Ogun zai garzaya.

A wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, Igboho ya ce ya samu labarin abubuwan da Fulani Makiyaya ke yi a jihar.

Yace: "Abinda mutane da dama basu sani ba shine Allah ya tashi tsiratar da mutanen Ibarapa daga hannun makiyaya, shi yasa naje wajen."

"Da ikon Allah, zamu magance sauran matsalolin dake jihar Ogun, dukkan Makiyaya masu kashe mutanen dake Ogun su shirya, ina nan tafe."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel