Na gama korar Fulani daga Oyo, jihar Ogun na nufa yanzu: Sunday Igboho

Na gama korar Fulani daga Oyo, jihar Ogun na nufa yanzu: Sunday Igboho

- Bayan tayar da hankalin Fulani a Ibarapa jihar Oyo, Igboho yace yanzu Ogun ya nufa

- Sifeto Janar na yan sanda ya bada umurnin damkeshi amma har yanzu ba'a yi ba

- Kungiyoyi Arewa sun yi alla-wadai da kokarin cin mutuncin Fulani da ake yi

Mai rajin kare rayukan Yarabawa, Sunday Adeyemo Igboho, ya bayyana cewa bayan samun nasaran fitittikan Fulani daga jihar Oyo, yanzu jihar Ogun zai garzaya.

A wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, Igboho ya ce ya samu labarin abubuwan da Fulani Makiyaya ke yi a jihar.

Yace: "Abinda mutane da dama basu sani ba shine Allah ya tashi tsiratar da mutanen Ibarapa daga hannun makiyaya, shi yasa naje wajen."

"Wahalan da mutanen Ibarapa ya bayyana ga jama'a bayan kisan Dr Aborede. Kisan mutumin ya tona asirin abubuwa da yawa dake faruwa a wajen."

"Da ikon Allah, zamu magance sauran matsalolin dake jihar Ogun, dukkan Makiyaya masu kashe mutanen dake Ogun su shirya, ina nan tafe."

Ya bayyana yadda wasu yan siyasa da yawa ke kokarin karya masa gwiwa duk da niyyarsa mai kyau.

"Na fi karfin wani ya bani cin hanci ko ya saye ni. Ba ni da yara a Najeriya da wani makiyayi zai sace, hakazalika babu wani makiyayin da ya isa ya tare ni," Igboho yace.

KU DUBA: Dangote: Yadda tsohuwar budurwata ta so 'warwarar' $5m daga wurina

Na gama korar Fulani daga Oyo, jihar Ogun na nufa yanzu: Sunday Igboho
Na gama korar Fulani daga Oyo, jihar Ogun na nufa yanzu: Sunday Igboho Photo Credit: Igboho
Asali: UGC

KU KARANTA: Ba abu bane mai sauki cika alkawuran da na dauka, in ji Buhari

A bangare guda, kungiyar kare mutuncin Arewacin Najeriya, Arewa Consultative Forum (ACF), ta bukaci gwamnatin kudu maso yammacin Najeriya da gwamnatin tarayya su dakatad da hare-haren da ake kaiwa Fulani da yankinsu.

ACF ta yi gargadin cew idan ba'a hana kai wadannan hare-hare kan Fulani ba, zai iya haddasa ramuwar gayya a Arewa kuma za'a iya maimata yakin basasan 1967, The Nation ta ruwaito.

A jawabin da kungiyar ta saki ranar Asabar, ACF ta ce abinda ya haddasa yakin 1967 shine hare-haren da aka rika kaiwa juna a kudu da Arewa kuma irin haka ya fara faruwa yanzu a kudu maso yamma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel