Cutar COVID-19: Mutane 22 sun mutu, 1,861 sun kamu ranar Laraba

Cutar COVID-19: Mutane 22 sun mutu, 1,861 sun kamu ranar Laraba

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa

- Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan dokar hukunta masu saba dokokin da NCDC ta kafa

A ranar Laraba, 27 ga watan Junairu 2021, Mutane 1,861 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Daga cikin wadanda aka sallama, akwai mutane 697 da sukayi jinya cikin gidajensu a Legas, 128 a Rivers da 116 a jihar Plateau.

Abin takaici, mutane 22 sun rasa rayukansu.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 126,160a Najeriya.

Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 100,365 yayinda 1,544 suka rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Jerin gwamnonin Najeriya 11 da suka kamu da cutar Coronavirus

KU KARANTA: Dangote: Yadda tsohuwar budurwata ta so 'warwarar' $5m daga wurina

A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan sabon dokan daurin watanni 6 a gidan kaso kan duk wanda aka kama yana saba dokokin kariya daga cutar Korona.

Shugaban kasan ya rattafa hannunsa dokar a Abuja, ranar Laraba.

Kamar yadda dokar killata, sashe 34 na sabon dokan ya tanada, duk wanda ya saba, za'a ci shi tara ko kuma yayi watanni shida a Kurkuku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel