Korona ta kashe mutane 77 cikin mako guda, sabbin mutane 1,617

Korona ta kashe mutane 77 cikin mako guda, sabbin mutane 1,617

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Kusan makonni biyu a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona kullum

- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce kawo yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya yanzu ya kai 112,004 cikin samfuri 1,172,234 da aka gwada.

Mutane 1,617 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Litinin, 18 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 112,004 a Najeriya.

Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 89,939 yayinda 1449 suka rigamu gidan gaskiya.

Ga jerin wadanda suka kamu a jihohi ranar Litinin:

Lagos-776

Kaduna-147

Kwara-131

FCT-102

Plateau-78

Edo-59

Ogun-53

Osun-45

Rivers-37

Taraba-36

Nasarawa-34

Adamawa-33

Kano-26

Delta-20

Ebonyi-16

Bayelsa-11

Gombe-11

Borno-2

Korona ta kashe mutane 77 cikin mako guda, sabbin mutane 1,617
Korona ta kashe mutane 77 cikin mako guda, sabbin mutane 1,617 Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

A bangare guda, ministar kudi da kasafin kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe N118.37 billion annobar Korona kadai a shekarar 2020.

Ministar ta bayyana hakan ne yayin jawabi a taron bayani kan kasafin kudin 2021, ranar Talata, 12 ga Junairu, Vanguard ta ruwaito.

A cewarta, an kashe N10.08 trillion kan gine-gine, biyan basussuka, biyan albashi da fansho da kuma wasu cefane a 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel