Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Gwamnan Borno Zulum

Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Gwamnan Borno Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Juma'a ya bayyana cewa domin adalci, ya kamata mulki ya koma kudu a shekarar 2023.

Ya soki maganganin cewa idan aka baiwa wani sashen kasar nan mulki zasu yi kokarin ballewa daga kasar.

Ya jaddada cewa akwai bukatar nuna adalci, saboda mayar da wani bangare saniyar ware ya sa suke neman ballewa daga kasa.

A jawabin da ya gabatar ranar Juma'a a Legas wajen taron tunawa da Cif Gani Fawehinmi, gwamna Zulum ya ce daya daga cikin hanyoyin da za'a samu cigaba a Najeriya shine nunawa ko wani bangare adalci.

Zulum yace: "Na yarda cewa a baiwa wasu bangarori damar shugabantar kasar nan a 2023."

KU KARANTA: Kimanin mutane 2000 suka kamu cutar Coronavirus ranar Juma'a, mafi yawa tunda Korona ta bulla

Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Gwamnan Borno Zulum
Kudu ya kamata mulki ya koma a 2023, Gwamnan Borno Zulum Hoto: @GovBorno
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel