Dan majalisa ya kamu da Korona bayan karban alluran rigakafi

Dan majalisa ya kamu da Korona bayan karban alluran rigakafi

- Duk ya ka karbi allurar rigakafin cutar, dan majalisar Republican ya kamu da Korona

- Kevin na daga cikin yan majalisar da suka ki yarda a rabawa mutane kudin tallafin Korona $2000

- Tuni ya shiga killace kansa kuma zai fara jinya gobe

Dan majalisar wakilan Amurka, Kevin Brady, ya bayyanawa duniya ranar Laraba cewa ya kamu da cutar Korona bayan karban rigakafin Pfizer-BioNTech na farko.

A ka'ida sau biyu mutum zai karbi alluran rigakafin makonni uku tsakani.

"Da daren nan, Likitan majalisa ya sanar da ni cewa na kamu da cutar COVID-19 kuma ina killace," ya bayyana a Tuwita.

"Kamar da yadda aka bada shawara, na karbi rigakafin Pfizer ranar 18 ga Disamba kuma ko a ranar sabuwar shekara na yi gwaji amma ban da cutar."

Yanzu haka an amince da amfani da rigakafin cutar Korona iri biyu a kasar Amurka. Na kamfanin Pfizer wanda ake karba sau biyu makonni uku tsakani, da kuma kamfanin Moderna, wanda ake karba sau biyu wata daya tsakani.

Dan majalisa ya kamu da Korona bayan karban alluran rigakafi
Dan majalisa ya kamu da Korona bayan karban alluran rigakafi
Source: Twitter

A bangare guda, hukumar da ke yaki da hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar da samun karin mutane 1,354 da suka harbu da annobar korona a ranar Talata, 5 ga watan Janairu.

An samu sabbin wadanda suka kamu ne a jihohi 22 inda Lagas wacce ta kasance cibiyar annobar a Najeriya ke kan gaba a yawan mutanen da suka kamu da cutar cikin kwana daya da mutum 712.

Sai kuma babbar birnin tarayya da ke bi mata inda ta samu karin mutum 145 da suka harbu yayinda Plateau, Kwara da Kaduna suka biyo baya da 117, 81 da 54 kowannensu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel