Makonni 53 da bullar Korona: Abubuwa 8 da ya kamata ka sani

Makonni 53 da bullar Korona: Abubuwa 8 da ya kamata ka sani

Kamar yadda ta saba saki mako-mako, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, ta saki rahoton inda aka kwana game da cutar Korona a Najeriya da duniya gaba daya.

A mako na 53, (27 ga Disamba zuwa 3 ga Junairu 2021)na bullar Korona , hukumar ta saki jerin abubuwa takwas da ya kamata ka sani, ga jerinsu:

1. A mako na 53, sabbin wadanda suka kamu da cutar ya ragu zuwa 5,733 daga 5,908 da suka kamu a mako na 52

2. A mako na 53, adadin wadanda aka sallama ya karu zuwa 4,010 daga 2,731 a mako na 52

3. Gaba daya, tun lokacin da cutar ta bulla, mutane 1,311 suka mutu sakamako

4. Adadin wadanda suka mutu a mako na 53 a fadin Najeriya 57

5. A mako na 53, adadin matafiyan da suka shigo Najeriya daga kasashen waje, 19,018, sabanin 19,238 da suka shigo a mako na 52

6. A mako na 53, adadin matafiyan da suka shigo Najeriya daga kasashen waje da suka kamu da cutar 62 ( banda na Legas)

7. A nahiyar Afrika, adadin wadanda suka kamu da cutar Korona kawo yanzu 2,830,462, kuma mutane 67,246 sun mutu

8. A duniya gaba daya, adadin wadanda suka kamu da cutar Korona kawo yanzu 83,322,449 kuma mutane 1,831,412 sun mutu

KU KARANTA: Gaskiya na gaji da boyewa, miji nike bukata - Kyakkyawar budurwa ta koka

Makonni 53 da bullar Korona a Nigeria: Abubuwa 8 da ya kamata ka sani
Makonni 53 da bullar Korona a Nigeria: Abubuwa 8 da ya kamata ka sani Credit: @NCDCgov
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hamshakiyar attajira, Sahoo Bint Abdullah Al-Mahboub, ta auri direbanta (Bidiyo)

A bangare guda, hukumar da ke yaki da hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar da samun karin mutane 1,354 da suka harbu da annobar korona a ranar Talata, 5 ga watan Janairu.

An samu sabbin wadanda suka kamu ne a jihohi 22 inda Lagas wacce ta kasance cibiyar annobar a Najeriya ke kan gaba a yawan mutanen da suka kamu da cutar cikin kwana daya da mutum 712.

Sai kuma babbar birnin tarayya da ke bi mata inda ta samu karin mutum 145 da suka harbu yayinda Plateau, Kwara da Kaduna suka biyo baya da 117, 81 da 54 kowannensu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel