Da duminsa: Allah ya yi wa tsohon ministan ilimi rasuwa

Da duminsa: Allah ya yi wa tsohon ministan ilimi rasuwa

- Allah ya yi wa tsohon karamin ministan ilimi, Farfesa Jerry Agada rasuwa

- Ya rasu a ranar Talata a asibitin gwamnatin tarayya da ke Makurdi, jihar Binuwai

- An haifa tsohon ministan a ranar 11 ga watan Nuwamban 1952 a karamar hukumar Ogbadibo

Tsohon karamin ministan ilimi kuma shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Binuwai, Farfesa Jerry Agada, ya rasu yana da shekaru 68 a duniya.

Kamar yadda rahotanni daga jaridar The Nation suka zo, Agada ya rasu a safiyar Talata a asibitin gwamnatin tarayya da ke Makurdi.

An haife shi a ranar 11 Nuwamban 1952 a Orokam da ke karamar hukumar Ogbadibo ta jihar Binuwai.

Tsohon marubuci ne kuma tsohon shugaban kungiyar marubata ta Najeriya (ANA).

KU KARANTA: Da duminsa: FG ta saka sabbin dokokin korona, jerin sunayen wurare 3 da ta rufe

Da duminsa: Allah ya yi wa tsohon ministan ilimi rasuwa
Da duminsa: Allah ya yi wa tsohon ministan ilimi rasuwa. Hoto daga @daily_nigerian
Source: Twitter

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel