Da duminsa: FG ta saka sabbin dokokin korona, jerin sunayen wurare 3 da ta rufe
- Gwamnatin tarayya ta saka sabbin dokoki a sakamakon yadda cutar korona ke yaduwa
-PTF ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta bukaci rufe dukkan mashaya, gidajen rawa da wuraren nishadi
- Ana bukatar dukkan jihohi 36 tare da birnin tarayya su bi sabbin dokokin na tsawo makonni biyar
Gwamnatin tarayya ta kakaba wasu sabbin dokoki yayin hauhawar yaduwar cutar korona a fadin kasar nan, Channels TV ta wallafa.
Boss Mustapha, wanda shine shugaban kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona, ya sanar da hakan a ranar Litinin bayan bayanin da yayi ga kwamitin a birnin Abuja.
Ya bayyana cewa wannan umarnin sun fito ne daga mashawarta inda aka mika su ga jihohi a kan a tabbatar da su na tsawo makonni biyar.
KU KARANTA: Ku mayar da kudin da kuka karba na gangamin #BringBackOurBoys#, Garba Shehu
Sabbin ka'idojin sun hada da rufe dukkan mashaya, gidajen rawa da wuraren taro. Rufe dukkan wuraren nishadi a dukkan jihohin kasar nan da birnin tarayya.
An bukaci dukkan gidajen cin abinci da su rufe ban da wadanda ke samar wa mazauna otal, wadanda ba a ci a ciki da kuma masu kaiwa har gida.
Hakazalika, dukkan tarukan da suka hada da biki, siyasa, nishadi, motsa jiki, liyafar karshen shekara da sauransu duk kada su wuce mutum 50.
Gwamnatin ta takaita tarukan addinai da kada a wuce kashi 50 na wurin bautar sannan a kiyaye dokokin nesa-nesa da juna tare da saka takunkumin fuska.
KU KARANTA: Alibaba, hadimin Ganduje ya bai wa Kwankwaso hakuri bayan tuhumar da ya sha kan kazafi
Kamar yadda Mustapha ya ce, duk wani taro da za a wuce mutum 50, toh ya zama dole a yi shi a budadden wuri.
Ya kara da cewa duk wasu nau'in sufuri dole ne su dauka rabin yawan fasinjojin da suke dauka domin biyayya ga dokar nesa-nesa da juna.
A wani labari na daban, gwamnonin da aka zaba a karkashin jam'iyyar APC sun bayyana sakankancewarsu a kan shugaba Muhammadu Buhari, sun ce suna da tabbacin zai kawo karshen rashin tsaron da ke addabar Najeriya.
Sun bayyana hakan ne yayin taya Buhari murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Sun bayyana hakan a wata takarda mai taken: "Fatan alheri ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari GCFR a ranar zagayowar haihuwarsa ta 78," wacce shugaban PGF, Abubakar Bagudu ya sanya hannu a Abuja, a ranar Alhamis.
A cewarsa, PGF tana taya shugaba Buhari, iyalansa da kuma 'yan Najeriya murnar cikar shugaban kasa shekaru 78 da haihuwa, jaridar The Punch ta wallafa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng