Bankin Duniya sunyi hasashen dogon matsin rugurgujewar tattali da yunwa
- Masanan Bankin Duniya sun fadi abin da zai faru da tattalin arzikin Najeriya
- World Bank Nigeria Development Update ta ce babu tabbacin za a tsira a 2022
- Yawan Talakawa zasu karu da miliyan 20, kuma za a iya yin yunwa nan gaba
Babban bankin Duniya ya yi wa Najeriya hasashen shekaru uku a cikin matsin lambar tattalin arziki muddin ba a dauki matakan da su ka dace ba.
Jaridar Daily Trust ta rahoto bankin Duniya ya na cewa muddin ba a cigaba da tafiya a kan dabarun ceto kasar ba, Najeriya za ta dade a matsala.
‘Nan da shekaru uku, akasarin ‘Dan Najeriya na iya ganin ci-bayan nasarorin cigaban tattalin da aka samu na shekaru, kuma kasar na iya fada wa cikin matsin da ya fi kowane tun 1980s.”
Jawabin da World Bank Nigeria Development Update (NDU) ta fitar dazu ya bayyana wannan.
KU KARANTA: Dalilin da ya sa aka shiga-aka fita, aka hana Buhari zuwa Majalisa
A cewar World Bank Nigeria Development Update, kasar na iya guje wa wannan matsala idan aka dage wajen bin manufofi da tafarkin da su ka dace.
An fitar da wannan bayani ne da taken: “Rising to the Challenge: Nigeria’s COVID-19 response”
Darektan babban bankin Duniya a Najeriya, Shubham Chaudhuri ya ce kasar tana cikin gaba mai wuya na daukar matakin da zai kai ta ga ci ko akasin haka.
“Babu tabbacin dawowa daidai a 2021, kuma hakan ya danganta da matakan da aka dauka.” Chaudhuri ya ce kila Talakawa su karu da miliyan 20 a 2022.
KU KARANTA: Shugaban kasa na cigaba da fuskantar matsin lamba a kan harkar tsaro
Hasashen yace za ayi fama da karancin abinci a lokacin da ake fuskantar annobar COVID-19 da karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwannin Duniya.
A jiya kun ji cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta ware makudan biliyoyin kudi domin aikin wasu hanyoyi a jihohin Filato, Kano, Kaduna da Abuja.
Ministocin tarayya sun bayyana jerin kwangilolin da gwamnatin tarayya a amince da su a taron FEC da aka yi a ranar Laraba, 9 ga watan 2020, a fadar Aso Villa.
Gwamnatin tarayya za ta fadada filin jirgin Maiduguri, sannan a gyara titin Kaduna-Jos.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng