Rashin tsaro: Jega, Falana, da su Yadudu sun ce a canza Shugabannin Sojoji

Rashin tsaro: Jega, Falana, da su Yadudu sun ce a canza Shugabannin Sojoji

-Wasu manyan mutane a kasar nan sun ce ya kamata a canza Hafsun sojoji

-Wadannan fitattu sun ce halin da ake ciki a yau ya cancanci a dauki mataki

-Tun 2015 aka nada hafsun sojoji, zuwa yanzu ana ta kiran canza su a kasar

A makon nan ne wani gungu na shahararrun mutanen Najeriya a karkashin wata kungiya ta ‘yan kishin kasa ta bukaci a canza shugabannin tsaro.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wannan kungiya ta Concerned Nigerians, ta na so a sallami hafsun sojoji saboda halin rashin tsaro da ake ciki.

A cewar wadannan mutane, al’umma su na cikin tashin hankali domin an gaza kawo karshen Boko Haram bayan shekaru 11 ana yaki da ‘yan ta’addan.

Bayan ‘yan ta’addan Boko Haram, ana fama da kashe-kashe daga hannun miyagu da ‘yan bindiga.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi ta'adi a Katsina

Wadanda su ke so ayi waje da hafsun sojojin su ne: Dr. Olisa Agbakoba, SAN; Prof. Jibrin Ibrahim, Bishof Matthew Hassan Kukah, Prof. Attahiru Muhammadu Jega, Funke Adekoya, SAN.

Akwai Prof. Joy Ngozi Ezeilo, Femi Falana, SAN; Rev Prof. Koyinsola Ajayi, SAN; Prof. Auwalu H. Yadudu, Mal. Yusuf Ali, SAN; da kuma Dr. Chris Kwaja.

Ragowar su ne: Chino Edmund Obiagwu, SAN; Father George Ehusani, Mr John Odah, Prof. Mohammed Tabiu, SAN; Mallam Kabiru Yusuf; da kuma Salisu Nuhu Mohammed.

Sai kuma Ledum Mitee. Ngozi Iwere, Ene Obi, Ms. Amina Salisu, Dr. Hakeem Baba Ahmed, Dayo Olaide, Danlami Nmodu, Dr. Udo Jude, Mallam Hamza Ibrahim, Prof. Ukachukwu A. Awuzie, Dr, Peter Ozo-Eson da Dr. Dipo Fashina.

“Ana kashe mutane kullum, ana yi wa mata fyade a kai-a kai, garkuwa da mutane ya zama ruwan dare. Manoma ba su iya zuwa gonakinsu.” Inji ‘yan kungiyar.

KU KARANTA: Inganta tsaro ya sa na rufe iyakokin kasa - Shugaba Buhari

Rashin tsaro: Jega, Falana, da su Yadudu sun ce a canza Shugabannin Sojoji
Shugabannin hafsun Sojoji Hoto: @BashirAhmaad
Source: Twitter

Har ila yau akwai Idayat Hassan, Abubakar Sokoto Mohammed, Prof. G.G. Darah, Prof. Adele Jinadu, Prof. Rufai Alkali, Rima Shawulu, Dr. Innocent Chukwuma, Dr. Kole Shettima, Candide-Johnson, SAN; Mal. Y.Z. Yau, Prof. Pat Utomi, A. B. Mahmoud, SAN; da Dr Usman Bugaje a jerin.

Su ka ce har Sultan ya fito ya na koka wa da halin da ake ciki a Najeriya. Shekaru fiye da biyar kenan da aka nada hafsun sojoji, har yau shugaban kasa bai canza su ba.

Ba wannan ne karon farko da jama’an kasar suka bukaci shugaban Najeriya Mai girma Muhammadu Buhari da ya dauki wannan mataki ba.

A makon nan kun ji cewa wasu ‘Yan fashi sun kutsa cikin gidan Gwamnan Akwa-Ibom da tsakar dare, sun saci miliyoyin kudi da aka ware domin a ba 'yan jarida.

Barayin sun haura gidan Gwamnatin ne bayan sun lalata kofar ofishin wani Hadimin gwamna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel