Trump ya bukaci magoya bayansa su hargitsa nasarar da Biden ya samu

Trump ya bukaci magoya bayansa su hargitsa nasarar da Biden ya samu

- Duk da ofishin shugaban kasa ya fara barinsa, har yanzu shugaba Donald Trump ya ki saduda cewa an kayar da shi a zabe

-Trump ya kekasa kasa, ya yi mirisisi, tare da yin tsaiwar gwamen jaki, a kan cewa shine ya lashe halastaccen zabe

- Tuni zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya fara shirin shimfida salon mulkinsa da zarar an rantsar da shi a watan Janairu

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, a ranar Laraba, ya gayawa magoya bayansa cewa sai sun yi aiki tuƙuru don kawar da sakamakon zaɓen Amurka da ya bawa abokin hamayyarsa, Joe Biden, nasara.

Trump ya yi iƙirarin cewa an tafka "maguɗi" a zaɓen don tabbatar da ɗan takarar Democrat, Joe Biden ya samu galaba a kansa.

KARANTA: Buhari ya yi wa wasu rukunin ma'aikata gata, ya dauke musu biyan haraji

"Ya zama dole mu kawar da wannan zaɓen", Trump ya fada a lokacin da ya kira magoya bayansa a Pennsylvania ta wayar tangaraho.

Trump ya bukaci magoya bayansa su hargitsa nasarar da Biden ya samu
Trump ya bukaci magoya bayansa su hargitsa nasarar da Biden ya samu
Asali: Getty Images

Fiye da sati uku kenan da Trump ya sha kayi a hannun Biden, ta hanyar bashi tazarar miliyoyin kuri'u, a wani salo da za'a iya bayyana wa da 'kayen Allah tsine uwar mai ƙarya'.

KARANTA: Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana dalilin zabge rabin albashin ma'aikata

"An tafka maguɗin zaɓe" a cewar Trump, inda ya yi ta kawo irin ƙulle-ƙulle da tuggun da aka shirya a wajen gudanar da zaɓuka a ƙasar.

Trump dai ya daɗe yana iƙirarin cewa an yi masa mamure tare da tafka maguɗi a zaɓen Amurka na bana, 2020, don ganin ya sha kayi, inda yace sam ba zai lamunci hakan ba.

Tun kafin a gudanar da zaben kasar Amurka, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa motar yaƙin neman zaɓen Biden/Harris ta tsaya cak a kan hanya a Pflugerville, wani gari a Texas, sakamakon harin da gungun magoya bayan Trump suka kai mata.

Lamarin ya jawo an dakatar da gudanar da yakin neman zaben Biden a lokacin saboda dalilan tsaro.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel