Buhari ya tsame rukunin wasu ma'aikata daga biyan haraji
- Muhammadu Buhari, shugaban kasa, ya ce gwamnatinsa ta bullo da tsari domin ragewa talakawaradadin hauhawar farashin kayayyaki
- A cewar Buhari, daga cikin tsare-tsaren akwai batun cire wa masu karbar mafi karancin albashi biyan haraji
- Sabon tsarin ya dace da tsarin shekarar 2019 na cire masu ƙananan sana'o'i daga biyan haraji wanda zai bunƙasa tattalin arziƙi
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta cire masu karɓar mafi ƙarancin albashi daga biyan harajin kuɗaɗen da suke shigo musu a wani mataki na ragewa talakawan Najeriya raɗaɗin hauhauwar farashin kayayyaki.
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a bayyaninsa wanda kuma mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, SAN, ya isar a ranar Litinin lokacin buɗe taron tattalin arziƙi karo na 26 mai taken "Haɗa hannu don tsira tare".
KARANTA: Zaria: 'Yan bindiga sun kai farmaki rukunin gidajen lakcarorin ABU, sun yi awon gaba da Farfesa
Shugaban ƙasar ya ce wannan yana ɗaya daga cikin shawarwarin shekarar 2020 na ƙudirin kuɗi, inda ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙi, da sauran tsara tsaren da aka aiwatar ko ake shirin aiwatarwa.
"Idan aka haɗa da sauran batutuwan shawarwarin ƙudirin, waɗannan tsare tsaren za su kawo tsira a tattalin arziƙin Najeriya ta hanyar motsa shi yadda ya kamata," a cewar shugaba Buhari.
KARANTA: NLC: Abin da ya fusata mu har muka fice daga tattaunawa da FG a kan karin farashin fetur
A cewar jawaban da babban mai bada shawara ta musamman akan ƴada labarai,ofishin shugaban ƙasar, Laolu Akande, shugaba Buhari ya ce;
"Muna shirin kawo sabon tsari wanda zai ware masu ɗaukar mafi ƙaranchin albashi daga biyan haraji.
"Wannan tsarin wanda ya dace da tsarin shekarar 2019 na cire masu ƙananan sana'o'i daga biyan haraji zai bunƙasa tattalin arziƙi.
"Kuma cikon alƙawarin da muka ɗauka ne don rage tsadar tafiye tafiye da kuma tasirin hakan wajen ƙara hauhawar farashin kayayyaki gun gama garin ƴan Najeriya," a cewarsa.
A ranar Lahadi ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta gama kammala tsare tsare don ganin ta zabge harajin motocin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje daga kaso 35% zuwa kaso 30%.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng