Majalisa tana tuhumar Lai Mohammed a kan N19m na tafiya da ya karba yayin kulle

Majalisa tana tuhumar Lai Mohammed a kan N19m na tafiya da ya karba yayin kulle

- Bayan Lai Mohammed ya gabatar da kasafin ma'aikatarsa na 2021 ne hukumar kididdiga ta fara yi masa tambayoyi na kure

-Ta ce ya aka yi ta ga yayi amfani da naira miliyan 19 lokacin kulle wanda aka ware musamman don tafiye-tafiyen kasashen ketare

- Ya amsa da cewa, sun yi amfani da kudaden ne kafin kullen COVID-19, wurin zuwa kasashe kamar Ingila da Spain don halartar taro daban-daban

A jiya ne Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed yayi bayani a kan kashe naira miliyan 19 wurin tafiye-tafiye lokacin kullen COVID-19.

Ya sha 'yar kure a lokacin da ya je gaban kwamitin gabatar da kasafin ma'aikatarsa na 2021, Daily trust ta ruwaito.

Wani mamba na kwamitin kasafi, Ezenwa Onyewuchi ya ce masa: "Bari in tuna maka abubuwan da kace a kan kasafin 2020. An baka naira miliyan 30 don tafiye-tafiye cikin kasa, kace ka kashe naira miliyan 23, an baka naira miliyan 96, ka kashe naira miliyan 90.

"Batun tafiye-tafiyen kasashen ketare, an baka miliyan 43, ka kashe miliyan 19. Ina mamakin yadda ka iya fita kasashen ketare a lokacin kulle, wanda aka hana kowa fita kasashen waje, har da za kace ka kashe naira miliyan 19."

Ministan ya amsa wannan tuhumar da cewa ya kashe naira miliyan 19 ne a tafiye-tafiyen kafin a kulle kasashe saboda COVID-19.

"Idan ka lura an yi kasafin naira miliyan 43 ne, amma kasa da kashi 40 bisa darin kudin muka kashe, saboda mun je taro daban-daban a kasashen ketare, tun daga taron UNWTO, UNESCO da aka yi a Spain da kuma Ingila. Mun yi wani taron na daban a Ingila duk kafin a kulle kasashe.

"Ina tunanin tafiyar da muka yi ta karshe ita ce wacce muka je Addis Ababa, inda muka raka shugaban kasa taron AU a wuraren watan Maris 2020 kafin kullen.

"Idan za ku tuna, karshen watan Maris ne akayi kullennan. Don haka duk abubuwan da muka kashe kafin kulle ne," Lai ya ce.

KU KARANTA: Babu gwamnatin da ta fattaki talauci kamar ta Buhari - Lai Mohammed

Majalisa tana tuhumar Lai Mohammed a kan N19m na tafiya da ya karba yayin kulle
Majalisa tana tuhumar Lai Mohammed a kan N19m na tafiya da ya karba yayin kulle. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Mbaka ga Buhari: Ka bai wa 'yan Najeriya hakuri a kan mulkin kama karya

A wani labari na daban, Gwamnoni 36 na Najeriya za su yi taro ranar 4 ga watan Nuwamba 2020 a kan yadda za su shawo kan matsalolin da ke addabar Najeriya, Daily Trust ta wallafa hakan.

Gwamnonin za su yi amfani da damar don tattaunawa a kan yadda za a yi da rundunar SARS da aka rushe, wadanda ayyukansu suka yi sanadiyyar zanga-zanga a cikin jihohin Najeriya.

Sannan za su tattauna a kan yadda aka wawushe kayan tallafin COVID-19 a ma'ajiyoyin gwamnati da ke jihohi daban-daban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel