Tsaro da satar kayan tallafi: Gwamnonin Najeriya za su yi muhimmin taro
- Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya za su yi taro ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba
- Za su yi taron ne don tattaunawa a kan matsalolin da ke addabar Najeriya don neman mafita
- Darekta janar na NGF, Asishana Bayo ne ya sanar da hakan, inda yace shugaban NGF ne zai yi jawabi
Gwamnoni 36 na Najeriya za su yi taro ranar 4 ga watan Nuwamba 2020 a kan yadda za su shawo kan matsalolin da ke addabar Najeriya, Daily Trust ta wallafa hakan.
Gwamnonin za su yi amfani da damar don tattaunawa a kan yadda za a yi da rundunar SARS da aka rushe, wadanda ayyukansu suka yi sanadiyyar zanga-zanga a cikin jihohin Najeriya.
Sannan za su tattauna a kan yadda aka wawushe kayan tallafin COVID-19 a ma'ajiyoyin gwamnati da ke jihohi daban-daban.
KU KARANTA: Gwamnonin Arewa sun sha alwashin tabbatar da hadin kan Najeriya
Darekta janar na NGF, Ashishana Bayo Okauru, ya ce shugaban kungiyar gwamnoni, gwamnan jihar Ekiti, Dr John Kayode Fayemi, zai yi jawabi a kan matsalolin da ke addabar Najeriya tun wan can taron da suka yi.
Okauru ya ce gwamnan jihar Ekiti zai tattauna da takwarorinsa na jihohi a kan yadda suka yi da fadar shugaban kasa a kan UBEC, don yanzu haka makarantu sun fara budewa a jihohi.
Ya ce Dr Fayemi zai yi magana a kan abubuwan da gwamnonin arewa suka tattauna a shagalin cikar Gidan AREWA shekaru 50 wanda aka yi cikin karshen mako wanda aka yi a Kaduna.
Kamar yadda darekta janar na NGF yace, ana bukatar ganin gwamnonin da misalin karfe 1 na rana, sannan za'a fara taron da misalin karfe 2:00 na rana daidai.
KU KARANTA: Jarabarsa tayi yawa, a taimaka min a raba mu - Matar aure a gaban kotu
A wani labari na daban, Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana yadda shugaba kasa Muhammadu Buhari yake kokarin samar wa matasa ayyukan yi, wanda ba a taba yin hakan ba a tarihin Najeriya.
A wani taron da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jagoranta a Kaduna, wanda shugabanni da manyan mutane da dama suka samu damar halarta, Mohammed ya sanar da shirin da shugaban kasar ya fara.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng