Babu gwamnatin da ta fattaki talauci kamar ta Buhari - Lai Mohammed

Babu gwamnatin da ta fattaki talauci kamar ta Buhari - Lai Mohammed

- Ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce tunda Najeriya ta kafu, babu shugaban kasan da ya tallafi matasa kamar Buhari

- Ministan ya fadi hakan ne a wani taron da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya jagoranta a Kaduna, wanda manyan mutane suka halarta

- Ya ce shugaban kasa ne kadai wanda ya taba ware kudade masu dumbin yawa don taimakon matasa da samar musu ayyukan yi

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana yadda shugaba kasa Muhammadu Buhari yake kokarin samar wa matasa ayyukan yi, wanda ba a taba yin hakan ba a tarihin Najeriya.

A wani taron da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jagoranta a Kaduna, wanda shugabanni da manyan mutane da dama suka samu damar halarta, Mohammed ya sanar da shirin da shugaban kasar ya fara.

Ministoci, Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da sauran manyan mutane sun halarci taron da aka yi a Kaduna.

A cewar ministan, shugaban kasa ya ce zai tsaya kai da fata don ganin ya taimaki matasa kuma ya kawar da talauci., Vanguard ta wallafa.

"Babu wata gwamnati da ta taba amfani da wannan salon kuma ta jajirce wurin kawar da talauci da samar wa matasa madafa kamar wannan" cewar ministan.

Ya tunatar da ware naira biliyan 75 da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wurin amfani dasu a shirin NYIF wanda aka yi musamman don matasa.

KU KARANTA: Bidiyon mutumin da aka hako yana numfashi bayan shekara daya da birne shi

Yace an ware kudin ne cikin naira tiriliyan 2.3 da za'ayi amfani dasu wurin daidaita tattalin arzikin kasa sakamakon COVID-19 don taimakon kananun kasuwanci a fadin kasar nan.

Babu gwamnatin da ta fattaki talauci kamar ta Buhari - Lai Mohammed
Babu gwamnatin da ta fattaki talauci kamar ta Buhari - Lai Mohammed. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Ministan ya ce a ranar 22 ga watan Yulin 2020, FEC ta amince da bayar da kudin don tallafawa matasa da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 35, kuma za'ayi hakan ne na tsawon shekaru 3, daga 2020 zuwa 2023.

NAN ta tunatar da lokacin da shugaban kasa yace fiye da mutane miliyan daya ne suka nemi tallafin NYIF da aka ware naira biliyan 75 tun bayan an bayar da adireshin yanar gizon a ranar 12 ga watan Oktoba 2020.

KU KARANTA: Sojan Najeriya ya zane budurwa a kan shigar banza, ya aske ladabtar da matashi saboda askin kansa

A wani labari na daban, tsohon shugaban hukumar kudin shiga (FIRS), Babatunde Fowler ya bayyana gaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC.

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da hakan ga jaridar Premium Times a ranar Litinin. Ya ce, "An gayyacesa zuwa hukumar kuma ya amsa kiran inda ya ziyarci ofishinmu da ke Legas."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng