Ngige ya ce za a iya la’akari da UTAS a madadin IPPIS wajen biyan Jami’o’i

Ngige ya ce za a iya la’akari da UTAS a madadin IPPIS wajen biyan Jami’o’i

- Gwamnati ta yi maganar yiwuwar karbar manhajar UTAS a madadin IPPIS

- An kama hanyar samun maslaha a yajin aikin da Malaman jami’an su ke yi

- Za a gabatar da UTAS a gaban AGF, NITDA, da NSA kafin a amince da manhajar

A ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, 2020, gwamnatin tarayya ta ce ta na duba yiwuwar karbar manhajar UTAS da kungiyar ASUU ta gabatar.

Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta gabatar da UTAS a gaban gwamnatin tarayya, a matsayin madadin manhajar nan ta IPPIS ta biyan albashin.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi la’akari da abin da ASUU ta zo da shi. Wannan sanarwa ya fito ne daga bakin Ministan kwadago, Dr. Chris Ngige.

KU KARANTA: Babu albashi ga wanda ba ya kan IPPIS - Buhari

Jaridar Premium Times ta bayyana cewa Chris Ngige ya bayyanawa ‘yan jarida wannan ne bayan zaman sa’a biyu da ASUU ta yi da majalisar dattawa.

Ngige ya ce a nan gida aka kirkiro manhajar da aka zo da shi, don haka ta cancanci a jarraba ta.

“Mun yarda bayan taron cewa mu yi la’akari da UTAS da aka zo da shi a madadin dabbakar da manhajar IPPIS da ke ta kawo mana matsaloli.” Inji sa.

Ngige ya ce: “Ba mu yi watsi da IPPIS gaba daya ba, kuma ba mu karbi UTAS kaco-kam ba.”

Ngige ya za a iya la’akari da UTAS a madadin IPPIS wajen biyan Jami’o’i
Shugabannin ASUU a taro Hoto: Punch.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari: Gwamnan Ribas ba ya goyon bayan yi wa Malamai karin albashi

“Matsayar da mu ka kai ita ce mu yi wa manhajar ASUU binciken tsa-tsaf. Za a gabatar da UTAS a ofishin babban akawun gwamnatin Najeriya a Laraba.”

Ministan ya ce daga nan za a kai wa NITDA manhajar domin ta duba, sai kuma a tafi NSA.

A farkon makon nan kun ji cewa Kungiyar ASUU ta yi wata ganawar sirri da shugabannin majalisar dattawa a game da sabaninsu da gwamnati.

Bayan zaman da aka yi, Ahmad Baba Kaita ya tabbatar da cewa ana neman kai ga maslaha.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel