Wasan sada zumunci: Muhimman 'yan wasan Najeriya 4 sun kamu da cutar korona

Wasan sada zumunci: Muhimman 'yan wasan Najeriya 4 sun kamu da cutar korona

- Super Eagles, kungiyarv kwallon kafa ta kasa, za ta buga muhimman wasannin sada zumunci guda biyu

- Najeriya za ta fafata da kasar Algeria ranar Juma'a sannan ta fafata da kasar Tunisia a ranar Talata mai zuwa

- Sai dai, sakamakon gwajin da aka sake yi wa 'yan wasan Najeriya a yau, Alhamis, ya nuna cew hudu daga cikinsu sun kamu da korona

A yayin da kungiyar kwallon kafa ta kasa 'Super Eagles' ke shirin wasan sada zumunci, 'yan wasa hudu sun kamu da cutar korona.

Najeriya za ta buga wasan sada zumunci da kasar Algeria ranar Juma'a sannan ta buga da kasar Tunisia ranar Talata.

Ana ganin hakan zai shafi kwazon kungiyar Super Eagles a wasannin da za ta buga.

Babban kociyan kungiyar Super Eagles, Gernot Rohr, ya ce 'yan wasan suna cikin yanayi mai kyau duk da ya ki bayyana sunansu.

DUBA WANNAN: Ta nan kudade su ke zirarewa: Majalisa ta shawarci Buhari ya soke wasu hukumomi

"Ba zan bayyana sunayensu ba duk da suna cikin yanayi mai kyau," a cewar Rohr.

An sake gwada 'yan wasan ne da ranar yau, Alhamis, gabanin wasan da za su buga gobe, Juma'a.

Wasan sada zumunci: Muhimman 'yan wasan Najeriya 4 sun kamu da cutar korona
Wasan sada zumunci: Muhimman 'yan wasan Najeriya 4 sun kamu da cutar korona
Asali: Twitter

A daren ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 155 a fadin Najeriya.

DUBA WANNAN: Sai Murna: Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Laraba 7 ga watan Oktoba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce mutanen 155 sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-84

Rivers-31

Kaduna-12

Osun-10

FCT-7

Oyo-6

Ogun-3

Kwara-2

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel