An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano

An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano

- Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano tayi nasarar ceto rayuwar mata 3, sai dai kash, mata daya ta rasa ranta

- Sabon ginin shagon bene da aka yi a kasuwar Kurmi, ya ruguzo wa mata 4 da suka je siye da siyarwa

- Al'amarin ya faru a ranar Asabar din da ta gabata, ya kai ga raunata mata 3 da kashe mace 1

Hukumar kashe gobarar jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wata mata sakamakon rushewar da wani sabon shago da ake ginawa a kasuwar Kurmi yayi.

Shagon ya fado wa mata 4 dake wucewa ta wurin ginin a ranar Asabar da ta gabata.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sa'idu Haruna, ya ce an kira su ta waya, inda aka sanar da su rushewar shagon.

"Jami'an mu sun nufi wurin cikin sauri, sun tarar da ginin ya fada wa mutane 4 , inda suka yi gaggawar kai su babban asibiti na Murtala Muhammad, sai aka tabbatar da mutuwar matar," cewar sa.

Wani mai gani da ido, Malam Jadda Bashir, ya sanar wa manema labarai cewa, duk wadanda ginin ya fada wa mata ne, sunzo siye da siyarwa.

Kamar yadda ya ce, sabon ginin bene ne aka yi, sai dai anyi rashin sa'a ya ruguzo.

Ya ce inda Allah yayi taimako ba a ranakun mako bane al'amarin ya faru ba, da wadanda zai shafa sai sun fi haka.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na yi nadamar taya Buhari kamfen a 2015 - Tsoho mai shekaru 80

An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano
An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: 2023: Ka taimakemu kada ka fito takara, za mu iya durkusawa gabanka - Fitaccen jigon Ibo ga Tinubu

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Adamawa sun damke wata matar aure da ake zargi da yi wa diyar mijinta dukan da yayi ajalinta.

Aishatu Umaru ta shiga hannun hukuma a ranar Alhamis bayan makwabta sun kai wa 'yan sanda koken zarginta da suke da kashe diyar mijinta mai suna Walida wacce take rikewa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje wanda ya zanta da manema labarai a Yola, ya tabbatar da kamen Aisha Umaru daga kauyen Kugama da ke karamar hukumar Mayobelwa ta jihar a kan laifin horo da yunwa da kuma kashe yarinyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel