Kotu ta raba auren shekara uku saboda katsalandan din surukai a rayuwar ma'aurata

Kotu ta raba auren shekara uku saboda katsalandan din surukai a rayuwar ma'aurata

- Katsalandan daga bangaren wasu surukai na daga cikin abubuwan da ke haddasa mutuwar

- Wata kotun gargajiya da ke zamanta a Ibadan ta raba auren shekara uku saboda irin wannan hali na shiga rayuwar ma'aurata

- Uwar Amarya ta yi zargin cewa uban Ango ya hana ma'aurata su yi rayuwarsu ta aure yadda suke so

A ranar Talata ne wata kotun gargajiya da ke zamanta a yankin Ile-Tuntun, jihar Oyo, ta raba wani auren shekara uku saboda katsalandan din uban miji a rayuwar auren dansa.

Uwargida Ibukun Amosun ce ta shigar kara a gaban kotun domin neman ta raba aurenta da mijinta, Babatunde, saboda tsangwamar da ta ke sha a wurin mahaifinsa.

A cewar Ibukun, surukinta ya gurbata zuciyar mijinta har ta kai ya yi watsi da al'amuranta.

Da ya ke zartar da hukunci a ranar Talata, alkalin kotun, Henry Agbaje, ya ce kotunsa ta raba auren ne domin a samu zaman lafiya.

Kazalika, ya gargadi tsofin ma'auratan su guji bijiro da duk wani hali da kan iya haifar da sabuwar rigima a tsakaninsu.

A cewar Ibukun, mazauniyar unguwar Apata a garin Ibadan, aurenta da Babatunde ya lalace ne saboda yawan tsangwamarta da mahaifinsa ke yi.

KU KARANTA KUMA: Yunƙurin fatattakar Oshiomhole daga APC: Jigon PDP ya roƙi APC ta ɗaga mashi ƙafa

Kotu ta raba auren shekara uku saboda katsalandan din surukai a rayuwar ma'aurata
Kotu ta raba auren shekara uku saboda katsalandan din surukai a rayuwar ma'aurata
Asali: Getty Images

"Ina da aikina mai kyau a Legas tun kafin na auri Babatunde Kuma mun kulla yarjejeniyar cewa zan cigaba da aiki bayan aurenmu.

"Amma bayan mun yi aure sai ya sanar da ni cewa sai na bar aiki, na dawo gida na yi zaman aure, ni kuma na nuna rashin amincewata.

"Haka na lallabashi har ya yarda ya barni na cigaba da aikina. Sai dai, hakan bai yi wa iyayensa dadi ba saboda duk lokacin da ya ziyarcesu sai ya sauya ra'ayi a kan maganar aikina.

"Wataran bayan na dawo daga wurin aiki sai na iske an sauya makullin gida. Da na kirashi na tambayi dalili sai ya sanar da ni cewa mahaifinsa ne ya bashi shawarar ya yi hakan.

"Bayan hakan, iyayensa sun yi watsi da yunkurin a sasantamu," kammar yadda Ibukun ta sanar da kotu.

Mahaifin Babatunde ya musanta zargin cewa ya umarci dansa ya rufe gidansa don kar Ibukun ta sake shiga.

"Mai girma mai Shari'a, ban umarceshi ya rufe mata gida ba, amma maganar gaskiya; ba zamu jurewa halayenta ba.

"Mu a al'adarmu, dole miji da mata su zauna tare, amma mahaifiyarta ta goya mata baya wajen kin zama da mijinta da kuma daukan juna biyu.

"Sannan ba ta shigar mutunci, ta na saka sutura kamar ba matar aure ba kuma haka ta ke fita babu ko kunya," a cewarsa.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun kashe 'yan banga a Jigawa

Babatunde bai halarci zaman kotun ba, mahaifinsa ne ya wakilce shi.

A nata bangaren, mahaifiyar Ibukun ta zargi mahaifin Babatunde da hana ma'auratan su yi rayuwarsu yadda suke so.

A wani labarin, Sohaib Ahmed mazaunin Rawalpindi ya siyawa matarsa fili a wata unguwa mai suna 'Sea of Vapour' a duniyar wata akan kudi dalar amurka arba'in da biyar ($45) a hannun hukumar duniya ta filayen duniyar wata.

Bayan Sushant Singh Rajput, jarumin fim din Indiya ya siyi filin a duniyar wata, shima dan Pakistan din yace baza'a barshi a baya ba, hakan ya sanya ya siyawa matar tasa a matsayin kyautar aure.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel