Tsohuwa 'yar shekara 57 da ta kammala JS3 na sakandare tace tana so ta zama ma'aikaciyar lafiya

Tsohuwa 'yar shekara 57 da ta kammala JS3 na sakandare tace tana so ta zama ma'aikaciyar lafiya

- Elizabeth Yamoah, mata ce mai shekaru 57 da haihuwa bata dade da rubuta jarabawar JSS ba, tace tanaso ta zama kwararriyar ma'aikaciyar jinya nan gaba

- Yamoah na neman taimako daga jama'a saboda ta samu ta wuce makarantar kwana da zarar jarabawar da ta rubuta ta fita

- Matar ta roki shugaban kasa Akufo-Addo ya nada ta shugabar dalibai ta SHS yadda zata samu damar wayar da kan al'umma akan ilimi

Wata mata 'yar kasar Ghana mai suna Elizabeth Yamoah, mai shekaru 57 da haihuwa wacce bata dade da gama rubuta jarabawar kammala firamare ba (BECE), ta ce tanaso ta zama cikakkiyar ma'aikaciyar jinya nan gaba.

Yamoah, wadda ta gama makarantar firamaren Odaoben Presbyterian ta ce tana da tabbacin sakamakon jarabawar ta zai yi kyau.

Tsohuwa 'yar shekara 57 da ta kammala JS3 na sakandare tace tana so ta zama ma'aikaciyar lafiya
Tsohuwa 'yar shekara 57 da ta kammala JS3 na sakandare tace tana so ta zama ma'aikaciyar lafiya
Source: UGC

Anan ne take cewa, tana rokon jama'a su taimaka mata da zarar jarabawarta ta fito kada ta tsaya wani jira ta fara makarantar kwana.

Jaridar Legit.ng ta tattara bayanannan daga Kasapaonline.com, inda aka ruwaito cewa Kasapa FM sunyi hira da Yamoah.

KU KARANTA: Tirkashi: Karamar yarinya ta sanar da mahaifinta yadda mahaifiyarta ke lalata da makwabcinsu idan baya nan

Ta kuma yi godiya ga shugaban kasa Akufo-Addo da ya sa karatun SHS ya zama kyauta, kuma ta rokeshi ya bata damar zama jagorar da zata dinga wayar da kan mutane akan amfanin ilimi.

Ta kara da cewa, a gaskiya taso karatu tun tana yarinya, amma wahalhalun rayuwa su suka sa ta bar makaranta tun a firamare.

Don haka, bazata taba cire rai ba, har sai burinta na cika kwararriyar ma'aikaciyar jinya ya cika, shiyasa ta koma makaranta.

Duk da mutane sunata yin maganganu marasa dadi, Yamoah ta ce bazata taba hakura ba har sai ta karasa karatunta.

Kamar yadda tace, manyan unguwa basu taimaketa ba gaba daya, sai ma sukar ta da sukai tayi har ta kusa hakura da karatun.

KU KARANTA: Budurwar da mahaifiyarta za ta mutu ta shirya aurenta cikin kwana 5, an daura aurenta a cikin asibiti

Shi kuwa fitaccen dan jarida na kasar Ghana wanda ke aiki da Citi rediyo, Umaru Sanda, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na sadarwa dake nuni da yadda rayuwar shi ta fara.

Sakamakon fitowa daga gida da basu da hali sosai, rayuwarshi ta yarinta ta kasance cike da kalubale, Sanda ya sha wahala sosai, inda yayi ta kokari wajen karatunshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel