Ma'aikacin jihar Jigawa ya rasu tare da 'ya'yansa da matarsa a hatsarin mota a hanyar Gaya-Dutse

Ma'aikacin jihar Jigawa ya rasu tare da 'ya'yansa da matarsa a hatsarin mota a hanyar Gaya-Dutse

- Hatsarin mota na daga cikin manyan abubuwan da ke jawo salwantar rayukan dumbin jama'a a fadin Najeriya

- Ana yawan alakanta yawan afkuwar hatsarin da rashin kyawun hanyoyin sufuri da ake dasu a sassan kasa

- Wani ma'aikcin gwamnatin jihar Jigawa ya rasu tare da matarsa da yaransu biyu a hanyarsa ta komawa wurin aiki bayan hutun karshen mako

Wasu mutane hudu 'yan gida daya sun rasu ranar Lahadi sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa dasu.

Hatsarin ya afku ne a yankin jihar Jigawa a kan babbar hanyar da ta ratsa ta karamar hukumar Gaya, jihar Kano, zuwa Dutse, wacce ta wuce har zuwa jihar Maiduguri.

Jarida Premium Times ta rawaito cewa hatsarin motar ya yi sanadiyyar rasuwar Abubakar Isah, mataimakin darekta ma'aikatar kasa ta jihar Jigawa, tare da matarsa da 'ya'ya biyu.

Da ya ke tabbatar da faruwar hakan, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, Abdu Jinjiri, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon karo da juna da motoci biyu suka yi da yammacin ranar Lahadi.

KARANTA: Makusanta shugaban kasa su na amfani da biyan tallafin man fetur don azurta kansu - Shugaban NNPC

Ibrahim Isyaku, dan uwa ga mamacin, ya shaidawa Premium Times cewa marigayi Abubakar ya na kan hanyarsa ta koma wurin aiki ne bayan hutun karshen mako da ya yi a jihar Kano.

Ya ce marigayin dan asalin karamar hukumar Birnin Kudu ne a jihar Jigawa.

Ma'aikacin jihar Jigawa ya rasu tare da 'ya'yansa da matarsa a hatsarin mota a hanyar Gaya-Dutse
Jami'an hukumar kiyaye hadura (FRSC)
Source: Depositphotos

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta ware kwanaki uku domin alhinin mutuwar marigayi sarkin Zazzau, Shehu Idris.

Muyiwa Adekeye, mai bawa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, shawara a harkar kafafen sadarwa ya fitar da sanarwa dangane da hakan.

A cikin sanarwar, wacce ta fito ranar Litinin, Mista Adekeye ya ce; "Za a bude ofisoshi a ranakun 21 da 22 ga watan Satumba, 2020.

KARANTA: Mamba a majalisar wakilai ya koma APC bayan gwamnan PDP ya fada ma sa bakar magana

"Akwai hutun aiki a ranar 23 ga watan Satumba domin karrama shi."

Sanarwar ta kara da cewa za a saukar da tutar Najeriya zuwa tsakiyar sandar karfe na tsawon kwanakin alhinin mutuwar Sarkin.

A ranar Lahadi, 20 ga Satumba, marigayi sarkin Zazzau ya rasu a wani asibitin sojoji da ke Kaduna bayan gajeriyar jinya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel