Zamfara: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 40

Zamfara: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 40

- Wasu 'yan bindiga masu tarin yawa sun kutsa kauyen Gobirawan Cali da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara

- Bayan damben da aka yi da wani dan bindiga da manomi har manomin ya samu nasara, sun koma daukar fansa

- Sun dinga harbe-harbe inda daga bisani suka tasa keyar manoma 40 na kauyen suka shige daji da su

A cikin ranakun karshen mako da suka gabata, wasu 'yan bindiga sun kai hari yankin Gobirawan Cali da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da manoma 40.

Wani mazaunin kauyen ya sanar da BBC cewa 'yan bindigan sun tsinkayi kauyen inda suka dinga harbe-harbe yayin da mazauna kauyen suka dinga gudu domin buya a daji.

Kamar yadda mazaunin kauyen yace, "Sun zo da tarin yawansu inda suka shiga yankin tare da fara harbe-harbe.

"Da yawanmu mun dinga gudu domin tsira. A halin yanzu babu jama'a a kauyen. Mun tsere daruruwanmu saboda sun dauke a ba-zata."

Wurin karfe uku na yamma 'yan bindiga sun shiga kauyen inda suka yi kokarin sace mutum daya. Ya yi dambe da daya daga cikin 'yan bindigan inda ya maka shi da kasa tare da kwace bindigarsa kirar AK 47.

KU KARANTA: Buhari ya tura wakilai Zaria, sun samu halartar jana'izar Sarki Shehu Idris

Zamfara: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 40
Zamfara: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 40. Hoto daga Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA: El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza

Yace, "Da gaggauwa ya dauke bindigar sannan ya wurga ta cikin wata gonar masara a kusa da shi. Dan bindigar ya farfado inda ya tsere.

"Bamu san cewa 'yan uwansa suna kusa ba. Daga nan sai suka fito da yawansu inda suka dinga harbe-harbe. Mun tsere amma sun sace manoma 40. Wasu dai a halin yanzu sun tsero.

"Mun kasa kiran jami'an tsaro saboda babu sabis. A yanzu yankinmu babu kowa kuma ba za mu koma ba har sai gwamnati ta samar mana da tsaro."

A wani labari na daban, runduna ta musamman ta sojin Najeriya da ke tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato, ta damke wani Hussaini Isah, wanda ta ce shine shugaban Sara-suka, wata kungiya da ta dade tana barna a yakin karamar hukumar Jos ta arewa.

Hakazalika, an cafke wasu mambobi 10 na kungiyar, Vanguard ta wallafa. Manjo janar Chukwuemeka Okonkwo, kwamandan rundunar ta musamman, wanda ya kai samamen a ranar Asabar a Jos, ya ce sun kama su a yankin Gangare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel