El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza

El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza

- Gwamna Malam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau

- Gwamnan ya bayyana cewa za a yi jana'izar basaraken da karfe 5 na yamma a garin Zazzau

- Ya bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na mika ta'aziyyarsa ga jama'ar Zazzau da jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, bayan gajeriyar rashin lafiya.

Sarkin ya rasu a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna a ranar Lahadi.

"Cike da alhini nake tabbatar da mutuwar baban jiharmu, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr, Shehu Idris Idris," El-Rufai ya wallafa a Facebook.

Ya kara da cewa, "Ya rasu a asibtin sojoji na 44 da ke Kaduna a yau bayan gajeriyar rashin lafiya. Za a yi jana'izarsa a garin Zazzau da karfe 5 Insha Allah.

DUBA WANNAN: Sultan Sa'ad Abubakar III ya nada sabbin hakimai 15 a Sokoto

"Za a kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona a yayin jana'izar da karbar makokinsa.

“Na sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan wannan babban rashin kuma yana mika ta'aziyyarsa.

"Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, zai jagoranci wakilan gwamnatin tarayya zuwa Zaria domin ta'aziyyar mai martaba a masarautar Zazzau da jihar Kaduna.

“Mun rasa babban abun alfaharinmu, mai cike da hikima sannan uban kowa. Allah ya bashi masauki a Aljanna Firdau. Amin"

DUBA WANNAN: Zaben Edo: Tattara komatsanka ka bar jihar Edo - 'Yan sanda ga Wike

El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza
El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

Tun da farko, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton Sarkin Zazzau, Mai martaba Alhaji Shehu Idris.

Majiyoyi da dama da suke da kusanci da fadar sarkin sun tabbatar da rasuwarsa a yau Lahadi.

Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Legit.ng cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.

"Tabbas Allah ya yi wa Sarki rasuwa. Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma'a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.

"Nan babu dadewa za a dawo da gawarsa Zaria domin fara shirin jana'izarsa," wata majiya mai kusanci da Iyan Zazzau ta tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel