Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon tambari (Hotuna da Bidiyo)

Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon tambari (Hotuna da Bidiyo)

- Daga cikin shirye-shiryen shagalin bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai, Buhari ya kaddamar da sabon tambarin kasar

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon logon ne a yayin taron majalisar zartarwa a ranar Laraba

- Kamar yadda sabon logon ya nuna, ya bayyana yadda Najeriya take kai hade a cikin shekaru 60 da tayi da samun 'yancin kanta

A yayin da Najeriya ke tunkarar cika shekaru 60 da samun 'yancin kai, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kaddamar da sabon logon kasar, wanda za a yi amfani da shi wurin shagalin bikin murnar zagayowar ranar samun 'yancin.

An kaddamar da sabon tambarin ne yayin taron majalisar zartarwa na tarayya da aka yi a Abuja, babban birnin kasar.

Ministocin tarayya da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne suka samu halarta, Channels TV ta wallafa.

Ministocin sun hada da ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, da sauransu.

A tun farko watan Satumban shekarar nan ne gwamnatin tarayya ta bukaci masu hazakar kirkire-kirkire da zane, da su kawo zane wanda za a yi amfani da shi a yayin da kasar ke cika shekaru 60 da samun 'yancin kai.

A kowacce shekara, ranar 1 ga watan Oktoba kasar Najeriya ke shagalin bikin zagayowar ranar samun 'yancinta.

Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna)
Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna). Hoto daga Channels TV
Source: Depositphotos

Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna)
Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna). Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

KU KARANTA: Babur Bura: Takaitaccen tarihi, aure, addini da yaren jama'ar kabilar

Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna)
Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna). Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna)
Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna). Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuka 8, gonaki sun kwashe a Katsina

Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna)
Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon Logon Najeriya (Hotuna). Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

A wani labari na daban, fitaccen marubuci Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauya salon mulkin Najeriya, ko kuma akwai yuwuwar dukkanmu za mu fada halaka.

Ya tabbatar da cewa, salon Najeriya babu shakka ba zai haifar da da mai ido ba.

Soyinka wanda ya sanar da hakan a wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar Talata, ya ja kunne a kan rabe-raben kan da ake samu a kasar nan wanda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayi magana a kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel