Katsina: 'Yan bindiga sun kashe Sarkin Tauri da wani mutum 1, sun sace mutane masu yawa

Katsina: 'Yan bindiga sun kashe Sarkin Tauri da wani mutum 1, sun sace mutane masu yawa

- 'Yan bindigar daji sun kutsa kauyen Daulai da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina inda suka kashe wani dattijo mai shekaru 50

- Sun kwashe mata, dabbobi, tare da kayan abinci duk a sa'o'in farko na ranar Litinin da ta gabata a kauyen

- A wani bangare, 'yan bindiga sun kutsa garin Dandume inda suka kashe Sarkin Tauri tare da sace matan aure hudu

Wasu 'yan bindiga sun kashe wani dattijo mai shekaru 50 mai suna Ashiru Aliyu a sa'o'in farko na ranar Litinin a kauyen Daulai da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Kamar yadda jaridar Katsina Post ta wallafa, 'yan bindigar sun sace mata masu yawa, sun kwashe dabbobi masu tarin yawa tare da kwashe kayayyakin abinci yayin harin.

'Yan bindigar sun isa kauyen wurin karfe 1:00 na dare kuma sun fara harbe-harbe babu kakkautawa.

A nan ne aka tabbatar da sun kashe rayuka biyu a take.

Hakazalika, wadanda ake zargin 'yan bindigar dajin ne, sun kashe wani basarake mai sarautar Sarkin Tauri na garin Dandume tare da garkuwa da wasu mutane hudu da suka hada da matan aure.

Lamarin ya faru wurin karfe 2 na daren ranar 14 ga watan Satumba, kamar yadda Katsina Post ta wallafa.

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce, 'yan bindigar da suka tsinkayi garin sun kai 30.

An gano cewa wasu daga cikin mazauna kauyen sun tsere harin ta hanyar fadawa daji tare da sauran yankunan da ke da kusanci da su.

KU KARANTA: Hoto: 'Yan sanda sun cafke matasa 4 a kan dukan dan sanda har ya mutu

Katsina: 'Yan bindiga sun kashe dagaci da wani mutum 1, sun sace mutane masu yawa
Katsina: 'Yan bindiga sun kashe dagaci da wani mutum 1, sun sace mutane masu yawa. Hoto daga Sahara Reporters
Source: Facebook

KU KARANTA: FG za ta kwaso 'yan Najeriya da ke gudun hijira a Nijar - Zulum

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga sun kwashe wasu matafiya da ke kan babbar hanyar Jibia zuwa Gurbi ta jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da su zuwa inda babu wanda ya sani.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta gano, a yayin da suke kan hanyar shiga daji da matafiyan, direban yayi yunkuri tserewa inda a take suka harbeshi suka bar shi a nan.

Majiyar ta kara da cewa, wasu mazauna kauyen ne suka tsinci direban bayan kwanaki biyu da aukuwar lamarin.

A nan ya sanar da jama'ar cewa, a kalla mutu 20 'yan bindigar suka yi garkuwa da su. A halin yanzu yana asbiti inda yake karbar taimakon likitoci.

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma yace mutum tara kacal aka sace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel