Bene ya rushe a Kano, ya kashe yara 2 'yan gida daya, mutum 8 sun jigata

Bene ya rushe a Kano, ya kashe yara 2 'yan gida daya, mutum 8 sun jigata

- Bene ya fada wa iyalan mutum daya a Gwammaja 'Yan Kosai a karamar hukumar Dala

- Mutum biyu sun rasu sakamakon hakan, yayin da sauran takwas suka samu raunika

- Kakakin hukumar kwana-kwana na jihar Kano, ya ce wurin karfe 1:30 aka kira su da dare

Wani bene ya rushe a sa'o'in farko na ranar Talata inda aka rasa rayukan mutum biyu kuma 'yan gida daya a Gwammaja 'Yan kosai, karamar hukumar Dala ta jihar Kano.

An gano cewa, mutum takwas duk a gida dayan sun samu miyagun raunika bayan sun kasa fitowa daga ginin da ya fadi.

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar Kano, Sa'adu Muhammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Vanguard. Ya ce Abdullahi Anas da Abdulmalik Anas sun riga mu gidan gaskiya.

Muhammed ya ce, "Mun samu kiran gaggawa daga wani Malam Abdullahi Muhammad daga Gwammaja 'yan Kosai a karamar hukumar Dala ta jihar Kano.

"Ya kira wurin karfe 1:30 na dare inda ya tabbatar da cewa wani gidan bene ya fadi."

"Bayan samun kira, mun gaggauta isa da kayan aiki wurin inda muka tara da iyalan a cikin mugun hali.

"An mika dukkan wadanda ginin ya fada musu asibitin Murtala Muhammad inda aka tabbatar da mutum biyu sun rasu," yace.

KU KARANTA: Baka damu da mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki ba - Kungiyoyi a Kano sun caccaki Buhari

'Yan sanda sun musanta farmakin da 'yan bindiga suka kai wa jirgin kasa a Kaduna
'Yan sanda sun musanta farmakin da 'yan bindiga suka kai wa jirgin kasa a Kaduna. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Edo 2020: Yadda wanda na gada ya dinga rantowa jihar kudi yana watanda da su - Obaseki

A wani labari na daban, masu taimako daga kasar Indiya sun tono wani yaro dan shekara hudu da rai daga cikin burbushin gini da ya danne shi tsawon kwana daya yana karkashi.

Mutane sunyi ta murna a ranar Talata 25 ga watan Agusta, bayan an toni yaron daga karkashin ginin da ya danne shi mai hawa biyar, bayan yaron, ginin kuma ya danne mutum 70 a wajen.

Lamarin dai ya faru a ranar Litinin 24 ga watan Agusta, a yammacin garin Mahad, dake kudancin Mumbai.

Sai da aka sanya ma'aikata da yawan gaske da kuma karnuka masu jiyo kamshin abu, inda suka yi ta aiki har zuwa cikin dare suna dauke da bulo da kwanika duka wajen neman wadanda ke da kwana a gaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel