Baka damu da mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki ba - Kungiyoyi a Kano sun caccaki Buhari

Baka damu da mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki ba - Kungiyoyi a Kano sun caccaki Buhari

- Kungiyoyin gammaya da ke jihar Kano karkashin KCSF ta caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Kungiyar ta kushe yadda aka kara farashin man fetur da kudin wutar lantarki a yayin da ake tsaka da annoba

- Waiya ya koka da yadda gwamnati ta ki tuntubar masu ruwa da tsaki yayin da za ta yi karin farashin

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu 130 karkashin jagorancin kungiyar hadin kan jihar Kano (KCSF), ta kushe karin farashin litar man fetur da kuma na kudin wutar lantarki a Najeriya.

Kungiyar ta caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da zama wanda bai damu da mawuyacin halin da 'yan kasar nan ke ciki ba, Daily Nigerian ta wallafa.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, shugaban KCSF, Ibrahim Waiya, ya caccaki gwamnatin tarayya a kan yadda farashin kayayyakin bukata suka yi tashin gwauron zabi ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki a fadin kasar ba.

Waiya ya kara da mamakin yadda gwamnati ta tabbatar da karin farashin man fetur duk da annobar korona da ta yi 'yan kasar illa.

"A game da wutar lantarki, sakamakon tuntubar masu ruwa da tsaki da aka yi a fadin kasar nan ya bayyana cewa kowa baya goyon bayan karin.

“A kowanne bangare, jama'a na kuka a kan halin da ake ciki ana tsaka da annobar korona, amma kuma gwamnatin ta cigaba da nuna halin ko in kula," yace.

"Wannan kukan da 'yan Najerya ke cigaba da yi a lokacin da ake tsaka da annoba da kulle abun takaici ne.

“Mun yadda da cewa, irin wannan karin zai sake lalata halin da jama'a suke ciki. A maimakon karin, da gwamnati ta bada tallafin rage radadi a kan annobar da ta addabi duniya," yace.

Shugaban ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta mayar da tsohon farashin a maimakon tsawwala wa 'yan Najeriya.

KU KARANTA: Mai sayar da burkutu ta yi wa ƴar sanda duka saboda N150,000, ta yaga mata kaya

Baka damu da mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki ba - Kungiyoyi a Kano sun caccaki Buhari

Baka damu da mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki ba - Kungiyoyi a Kano sun caccaki Buhari. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Dalilinmu na yin taro da Obasanjo, Afenifere da sauransu - Dattawan arewa

A wani labari na daban, Malam Garba Shehu, babban mai bai wa shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, shawara a fannin yada labarai, ya ce gwamnatocin da suka shude basu da karfin guiwar daukar matakan da suka dace.

A wata takardar da Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce za a tuna da shugaban kasa Muhammad Buhari ko nan gaba, a matsayin shugaban da ya bada "gudumawa ga habakar tattalin arziki da ci gaban kasar nan, tare da kawo karshen dukkan wata rashawa da ke tattare da tallafin man fetur."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel