Mun gaji da jan kafa da ka ke yi, ka canja shugabannin tsaro: Hadakar kungiyoyin arewa ga Buhari

Mun gaji da jan kafa da ka ke yi, ka canja shugabannin tsaro: Hadakar kungiyoyin arewa ga Buhari

Haɗakar dattawan arewa ta tsakiya, CNCE, ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugabannin hukumomin tsaro game da ƙallubalen tsaro a ƙasar.

Dattawan sun ce sun zabi Buhari ne saboda kwarewarsa a matsayin sa na shugaban mulkin soja saboda haka suna sa ran ya ba wa maraɗa kunya.

Hare-hare daga kungiyoyi kamar Boko Haram da yan bindiga ya yi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi da dama a ƙasar.

Mun gaji da jan kafa da kake yi, sallami shugabannin tsaro: Hadakar kungiyyin arewa ga Buhari
Mun gaji da jan kafa da kake yi, sallami shugabannin tsaro: Hadakar kungiyyin arewa ga Buhari. Hoto daga Ripples Ng
Source: Twitter

Sakamakon haka, ƴan Najeriya da dama ciki har da ƴan Majalisa sun matsa wa shugaban kasar lamba ya dauki mataki a kan lamarin ciki har da canja shugabannin tsaron.

DUBA WANNAN: Mutum 4 ƴan gida ɗaya sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin, Hadaƙar ta ce babu wani yanki na Najeriya da ba a samun harin ƴan ta'addan inda suka ƙara da cewa ƴan Najeriya sun gaji da dalilai marasa tushe.

"Mun bi sahun ƴan Najeriya da dama wurin kira ga shugaban ƙasa ya yi wa tsarin tsaron ƙasar nan garambawul ta hanyar sallamar shugabannin hukumomin tsaro a matsayin mataki na farko," in ji sanarwar da shugaban CNCE, Usman Bida ya fitar.

"Ƴan Najeriya sun gaji da zaƙin baki da alƙawurran cewa abubuwa za su dai-daita a bangaren tsaro.

"Muna baƙin cikin ganin cewa babu wata jiha a arewa maso tsakiya da yan ta'adda ba su kai hari, yankin da a baya shine ya fi dukkan sauran zaman lafiya a dukkan arewa."

Haɗakar ta ce har yanzu tana cikin fargaba game da kama yan ta'adda fiye da 400 da muggan makamai a jihar Nasarawa kwatsam kuma sai hukumar Kwastam ta sanar wa ƙasar cewa ƴan ta'adda sun ratsa wasu yankunan arewa maso tsakiya.

"A halin da muke ciki a yanzu, ƴan Najeriya da dama a arewa ta tsakiya da wasu yankunan suna cikin tashin hankali saboda wannan sanarwar," in ji shi.

KU KARANTA: Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

"Wasu yankunan Nasarawa, Niger da Kogi ba su shiguwa saboda yan ta'adda, masu garkuwa da mutane da ƴan fashi da ke cin karen su ba babbaka.

"Mun zaɓi Buhari ne saboda kwarewarsa a fanin tsaro da rikon gaskiya kuma muna sa ran ya taɓuka abin azo a gani.

"Shugaban Kasa, muna tare da kai kuma za mu cigaba da goyon bayan ka amma muna ganin rashin canja shugabannin tsaron tsawon shekaru biyar duk da ƴan Najeriya sun nuna a canja su yana kawo cikas ga sojoji. Muna kira gare ka ka ɗauki mataki yanzu.

"Shugaban ƙasa, Babu yadda za ayi jami'ai huɗu su fi dubbai da muke da su a rundunar sojojin. Wannan shine dalilin da yasa muke kira gare ka cikin gaggawa ka canja su."

A wani rahoton, kun ji cewa a ƙalla hausawa 2 mazauna Oyigbo a ƙaramar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers ne suka mutu sakamakon harin da wasu da ake zargin ƴan kungiyar masu fafutikan kafa ƙasar Biafra, IPOB, suka kai musu a Oyigbo.

Wani ganau ya bayyana cewa fusatattun mambobin na ƙungiyar IPOB sun kai wa Hausawa mazauna Oyigbo hari a ranakun Asabar da Lahadi.

Ganau ɗin ya ce an kashe aƙalla mutane biyu yayin da wasu da dama sun samu munannan raunuka kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel