An bawa gwamnan jihar Zamfara babbar sarauta a kudancin Najeriya

An bawa gwamnan jihar Zamfara babbar sarauta a kudancin Najeriya

Sarkin Ife, Adeyeye Enitan Ogunwisi Ojaja II, ya bada sarautar "Obapero na Ife-Odua' ga gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle

A wata sanarwa da mai bawa bawa gwamnan shawara a fannin sadarwa, Zailani Bappa, sarautar wacce take nufin 'mai samar da zaman lafiya' za a bayar da ita ga gwamnan a mako mai zuwa.

Sanarwar ta bayyana cewa Sarkin ya bayyana bada sarautar a lokacin da ya kaiwa gwamnan ziyara a gidanshi dake Abuja ranar Alhamis.

An bawa gwamnan jihar Zamfara babbar sarauta a kudancin Najeriya
An bawa gwamnan jihar Zamfara babbar sarauta a kudancin Najeriya
Source: Facebook

"Ya bayyana kokarin gwamna Matawalle, inda ya bayyana shi a matsayin gwamnan da baya nuna kabilanci, ya ce kyawun halin shi ne ya sanya ya samu nasarar da yake da ita a yanzu.

"Ya ce halayen Matawalle na shugabanci ya kamata kowanne gwamna yayi koyi da su a Najeriya, saboda ba wai ya nuna cewa shi shugaba na kwarai bane, ya kuma samar da tsaro a jihar.

"Ya ce shirin da gwamna Matawalle yake na farfado da ma'adanai a jihar abu ne mai kyau wanda zai kawo cigaba a Najeriya."

KU KARANTA: Ganduje ya biya naira miliyan 257 don daukar nauyin dalibai 43 su tafi karatu kasar Misra

Da yake martani akan wannan mukami da aka bashi, gwamna Matawalle, ya nuna godiyarshi ga sarkin akan wannan mukami da ya bashi, inda yayi alkawarin zuwa Ife a cikin kwanakin nan.

Ya ce: "Da wannan sabon shirye-shirye na farfado da ma'adanai da gwamnatinsa za ta yi, jihar Zamfara nan da wasu 'yan watanni za ta zama abin kwatance a cikin jihohi masu arziki a Najeriya.

Yayi alkawarin yin bakin kokarinsa wajen cigaba da shugabanci nagari, sannan yayi alkawarin sako talakawa a gaba a kowanne abu da zai yi a jihar kafin nan zuwa karshen mulkinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel