Mutumin da ya shekara 80 bai yi aski ba ya ce yana ganin zai mutu ne duk ranar da yayi aski

Mutumin da ya shekara 80 bai yi aski ba ya ce yana ganin zai mutu ne duk ranar da yayi aski

- Nguyen Van Chien, yana da abin bauta guda bakwai, kuma imanin da yayi ya hana shi cire duk wani abu da aka haifeshi da shi

- Chien ya ce yayi imanin idan ya aske gashin sa ko ya wanke, to tabbas zai mutu

- Tsohon mai shekaru 92 ya bayyana cewa hatta taje kanshi baya yi, kawai yana nade shi acikin rawani ne dan yaji dadin tafiya.

Wani mutumi mai suna Nguyen Van Chien, mai shekaru 92 daga kasar Vietnam dake yankin Kudu maso Gabashin Asia, ya dauki lamari akan rashin aski da gaske.

Tsohon ya ce addininsa bai kyale shi ya cire wani abu da aka haife shi da shi ba, saboda haka yanzu shekarar shi 80 bai shiga shagon mai aski ba.

A cewar Van, bai kuma wanke gashin kan shi din ba tsawon shekaru 80 saboda yana tsoron zai mutu idan ya wanke.

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda giwa ta kaiwa wani mutumi da yake tafiya a keke hari ta kwace keken shi

Tsohon ya bayyanawa manema labarai cewa yana nade gashin kanshi ne da kyalle a duk lokacin da yake so ya fito cikin tsafta.

Ya kara da cewa bai isa yayi amfani da mataji ya taje kanshi ba, ko kuma ya canjawa gashin nashi launi, saboda hakan ya sabawa abubuwan bautar shi guda bakwai.

"Nayi imanin idan nayi aski zan mutu ne. Haka ya sanya ko tajewa bana yi," ya ce.

Van ya ce a lokacin da yake makaranta, an taba umartar shi ya aske gashin kanshi, amma saboda hakan ya sabawa addininshi ya sanya ya bar makarantar bai kara komawa ba.

Haka dan da ya haifa shi ma ya dauko halinsa, inda yace ya taba ganin wani ya mutu a lokacin da yayi kokarin canja yanayin gashin kanshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel