Boko Haram: Dahiru Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa

Boko Haram: Dahiru Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa

- Fitaccen Malami Sheikh Dahiru Bauchi, ya tsame kansa daga ikirarin da ke fitowa daga Mailafia na cewa yana goyon bayansa

- Bayan kwashe sa'o'i a ofishin hukumar DSS a karo na uku, Mailafia ya ce fitattun jama'a a kasar nan har da shehin malamin suna goyon bayan ikirarinsa

- Sai dai Malamin ya ce ko jaje bai taba hada shi da Mailafia ba balle ya goyi bayan cewa gwamnan arewa ne kwamandan Boko Haram

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a ranar Laraba ya musanta goyon bayan ikirarin tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafia, wanda yace wani gwamnan arewa shine kwamandan Boko Haram.

A wata tattaunawa da Malamin yayi da jaridar Daily Trust a ranar laraba, Dahiru Bauchi mai shekaru 93, ya ce bai tura sakon goyon baya ko jaje ga Mailafia ba ko bayan da yayi hira da wani gidan rediyo a kan kashe-kashen kudancin Kaduna da kuma Boko Haram.

Sau uku hukumar tsaro ta fararen kaya ta gayyaci Mailafia domin amsa tambayoyi a ofishinta da ke jihar Filato.

A yayin zuwansa na karshe a ranar Litinin, 14 ga watan Satumban 2020, bayan tattaunawa da jami'an tsaron na farin kaya, Mailafia ya sanar da malamai, lauyoyi da 'yan jaridu cewa, fitattun jama'a a kasar nan suna goyon bayansa.

"Na samu sako daga manyan malaman addinin Islama da suka hada da Sheikh Dahiru Bauchi.

"Ya turo min sakon inda yake bayyana cewa yana yi min addu'a," Mailafia yace yayin tattaunawa.

"Matasan Musulmi suna goyon bayana. Suna yi min addu'a. Sun yadda cewa ni ne muryarsu, hakazalika matasan Kiristoci," yace.

KU KARANTA: Motocin kudin da ka kwamushe a gidanka ba za su iya siya maka Edo ba - Ikimi ga Tinubu

Boko Haram: Dahiru Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa
Boko Haram: Dahiru Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan daba sun kai wa tawagar Gwamnan APC hari, sun ragargaza ababen hawa

Amma kuma, Sheikh Dahiru Bauchi, wanda yake daya daga cikin manyan jiga-jigan darikar Tijjaniya wanda ke da miliyoyin mabiya a Najeriya da sauran sassan duniya, ya ce bai yi magana da kowa ba, kuma bai aike kowa wurin Mailafia ba.

"Idan dai Mailafia ne wanda ya yi mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya lokacin da Sanusi Lamido Sanusi yake gwamnan, tabbas na yi musu addu'ar nasara a lokacin suna bankin, kuma saboda Sanusi ne," tsohon yace bayan kallon bidiyon tattaunawa da Mailafia.

"Amma kuma ikirarinsa da zarginsa a kan gwamnonin arewa, bana tare da shi kuma ban aika wani wurinsa ba," yace.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi addu'ar zaman lafiya da daidaituwa a Najeriya, kuma ya shawarci Musulmi da su nemi yafiyar Allah da kuma daidaituwar kasar nan.

A wani labari na daban, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailafia, ya ce rayuwarsa tana cikin garari tare da hatsari.

Mailafia ya sanar da hakan ne a yayin da yake martani a kan gayyatar da jami'an tsaro na farin kaya suka yi masa a karo na uku.

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin, a wata takarda da ya fitar a Jos a ranar Juma'a, ya kwatanta gayyatar DSS da siyasa. Ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su yi masa addu'ar kariya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel