Yanzun-nan: Mutane da dama sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a Ondo

Yanzun-nan: Mutane da dama sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a Ondo

- Rahotanni sun nuna cewa an rasa rayuka da yawa a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Ondo

- Mummunan al’amarin ya afku ne a yankin Ikare-Akoko da ke jihar a ranar Asabar, 29 ga watan Agusta

- Wani direban babban mota ne ya rasa daidaita tuki inda ya je ya daki shaguna a tsakanin yankin sannan ya jikkata mutane da dama

Mutane da dama ake zaton sun mutu yayinda wasu da dama suka ji munanan raunuka biyo bayan wani hatsari da ya afku sanadiyar kwacewar wata babban motar man diesel sannan ta afka wani yankin kasuwanci a unguwar Oloko, Ikare Akoko, jihar Ondo.

Wani idon shaida ya bayyana wa Sahara Reporters cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Asabar, 29 ga watan Agusta.

Yanzun-nan: Mutane da dama sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a Ondo
Yanzun-nan: Mutane da dama sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota a Ondo
Asali: UGC

Ya ce direban babban motan ya gaza daidaita motar sannan ya je ya hade da shaguna a yankin.

Wani idon shaida ya ce an dauki wadanda suka ji rauni zuwa asibitin kwararru na jihar a garin da kuma cibiyar jinya ta tarayya da ke Owo.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya barke a kasar Sweden sakamakon shirya taron kona Al-Kur'ani da wasu sukayi

A gefe guda, mun ji cewa wasu mutum uku da aka bayyana a matsayin Melody M, Isaac G., da James S., sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a jihar Adamawa.

Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa mutanen, wadanda suka kasance maza biyu da mace guda, sun nitse ne a yayinda suke a hanyarsu ta zuwa bikin binne wani a karamar hukumar Lamurde bayan kwale-kwalen ya kife.

Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban karamar hukumar Lamurde, Burto Williams, ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki.

“Hatsarin abun bakin ciki ne da yake bukatar gwamnati ta kawo agaji ga mutanen yankin wadanda ruwa ke yawan yi wa barna.

KU KARANTA KUMA: Idan dan kabilar Igbo ya zama shugaban kasa a 2023 za a ga canji - Ohanaeze Ndigbo

“Karamar hukumar Lamurde na kokarin samar da kulawar likitoci ga wadanda suka tsira yayinda hukumar za ta dauki nauyin birne mutum uku da suka mutu,” in ji Burto.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng