Yanzu-yanzu: Babban basaraken jihar Kogi ya rasu

Yanzu-yanzu: Babban basaraken jihar Kogi ya rasu

- Allah ya yi wa Micheal Ameh Oboni rasuwa

- Har zuwa mutuwarsa, ya kasance Attah na Igala, shugaban kungiyar sarakunan gargajiya na jihar Kogi

- A halin da ake ciki, mahukunta basu fitar da sanarwa a kan mutuwar ba

Al’umman jihar Kogi sun yi babban rashi yayinda Attah na Igala, shugaban kungiyar sarakunan gargajiya na jihar, Dr Micheal Ameh Oboni ya mutu.

Basaraken ya mutu ne a Abuja a ranar Laraba, 26 ga watan Agusta, a wani asibiti mai zaman kansa, jaridar Tribune ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Babban basaraken jihar Kogi ya rasu
Yanzu-yanzu: Babban basaraken jihar Kogi ya rasu
Asali: UGC

A cewar jaridar, a daidai lokacin kawo wannan rahoton, gwamnatin jihar Kogi da majalisar gargajiya na Igala basu fitar da kowani jawabi ba a kan mutuwar basaraken.

KU KARANTA KUMA: Abin alfaharinmu: Harshen Hausa ya zamo yare mafi saurin yaduwa a duniya

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamnan jihar Jigawa na farko a mulkin soji, Olayinka Sule, ya rasu ranar Lahadi yana da shekaru 72 a duniya.

Sule, tsohon birgediya janar a rundunar sojin Najeriya, ya zama gwamnan jigawa na farko bayan kirkirar jihar a watan Agusta na shekarar 1991 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Ya jagoranci gwamnatin jihar har zuwa watan Janairu na shekarar 1992, lokacin da ya mika mulki zuwa gwamnatin farar hula ta farko a Jigawa a karkashin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Barista Ali Sa'ad BirninKudu, lokacin janhuriya ta uku.

Gwamnan jihar Jigawa na biyu a janhuriya ta hudu, Sule Lamido, ne ya sanar da mutuwar marigayin Sule a cikin wani jawabi da kakakinsa, Mansur Ahmad, ya fitar.

Sule Lamido ya bayyana marigayi Sule a matsayin dattijon arziki da ba za a maye gurbin rashinsa ba.

Ya yi addu'ar Allah ya ji kansa, ya yi masa sakayya da gidan Aljannatul Firadus.

A dan takaitaccen lokacin da ya shugabanci jihar Jigawa, marigayi Sule ya saka tubalin aiyukan raya garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, da suka hada da saka tubalin fara gina gidaje 1000 a unguwannin Takur da Yadi.

Marigayi Sule ya taba rike babban kwamanda (GOC) a barikin soji ta farko da ke Kaduna a 1996, shekarar da ya yi ritaya daga aikin soja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel