Gangar siyasar 2021: An fara shirye-shiryen zaben kananan hukumomi a jihar Kano

Gangar siyasar 2021: An fara shirye-shiryen zaben kananan hukumomi a jihar Kano

- Hukumar zabe ta jihar Kano ta bada sanarwar tuni ta fara shirye-shiryen gabatar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar wanda za ayi a cikin shekarar 2021 mai zuwa

- Shugaban hukumar na jihar Farfesa Garba Ibrahim Sheka, shine ya bayyana haka a ranar Laraba

- Ya ce hukumar za tayi iya bakin kokarinta wajen ganin an gabatar da zabe cikin adalci a fadin kananan hukumomi 44 na jihar

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta reshen jihar Kano (KANSIEC) ta ce tuni ta fara gabatar da shirye-shiryen zaben kananan hukumomi da za a gabatar a jihar a shekarar 2021.

Shugaban hukumar na jihar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka, shine ya bayyana haka a ranar Laraba a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar bada shawara ta (IPAC), ya kara da cewa hukumar za ta tafi da duka jam'iyyun siyasa.

Gangar siyasar 2021: An fara shirye-shiryen zaben kananan hukumomi a jihar Kano
Gangar siyasar 2021: An fara shirye-shiryen zaben kananan hukumomi a jihar Kano
Asali: Facebook

Sheka ya ce jinkiri da ake samu a baya daga hukumar da kuma rashin kayan aiki da aka samu a zaben da aka gabatar a shekarar 2018 duka an gyara wadannan.

Ya bayyana hakane a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta jihar Dahiru Lawan Wambai, inda ya ce sun riga sun gama shirye-shirye tsaf wajen gabatar da wannan zabe, kuma hukumar za tayi kokari wajen ganin anyi zabe cikin adalci.

KU KARANTA: Sunaye: Jam'iyyar PDP ta ware kwamiti ta mutum 145 da zasu yi yakin neman zaben gwamnan jihar Ondo

Shugabar hukumar IPAC na jiha, Isa Nuhu Isa, ya tabbatar da goyon bayan kungiyarsu wajen gabatar da wannan zabe cikin adalci.

Daily Trust ta ruwaito cewa a cikin watan Yuli ne gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya fara gabatar da gyare-gyare a cikin jam'iyya mai mulki cikin kananan hukumomi 44 na jihar yayin da zaben ke kara karatowa.

Sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Abba Anwar, ya bada sanarwar cewa gwamnan tuni ya hada wasu kwamitoci da za su je duka kananan hukumomin jihar domin kara inganta abubuwa da kuma kokarin mambobin kungiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel