Buhari ya bayyana muhimman ayyuka 9 da gwamnatinsa za ta sa gaba nan da shekaru 3

Buhari ya bayyana muhimman ayyuka 9 da gwamnatinsa za ta sa gaba nan da shekaru 3

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya bayyana bangarorin da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a cikin shekarun da suke rage masa na mulki don inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Buhari ya yi jawabin hakan ne bayan wasikar jinjina da ya samu daga jakadun kasashen Algeria, Vietnam, Tanzania, Cote d’Ivoire, Chad, Somalia, jamhuriyar Sahrawi Arab da Iran.

A cewar shugaban kasar: "A kokarinmu na cimma tsayayyun dokoki na cikin gida da waje tare da habakar kasar nan, mun gano cewa bai wa bangarori tara fifiko zai bamu alkibla a cikin shekaru kadan da suka rage mana na mulkin kasar nan."

Ya bayyana cewa zai mayar da hankali wurin:

1. Tabbatar da wanzuwar tattalin arziki mai habaka da daidaituwa.

2. Fattakar talauci.

3. Fadada bangaren noma da kiwo don samun tsaro ta bangaren abinci .

4. Samun wutar lantarki tare da inganta sauran ababen more rayuwa.

5. Fadada ci gaban kasuwanci, dogaro da kai da masana'antu.

6. Fadada hanyoyin samun ingantaccen ilimi.

7. Ingantattun cibiyoyin lafiya na zamani ga 'yan Najeriya

8. Kafa tsari na musamman na yaki da rashawa da ingantaccen mulki.

9. Tabbatar da tsaro ga dukkan 'yan Najeriya.

Buhari ya bayyana muhimman ayyuka 9 da gwamnatinsa za ta sa gaba nan da shekaru 3
Buhari ya bayyana muhimman ayyuka 9 da gwamnatinsa za ta sa gaba nan da shekaru 3. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Bayan karbar albashi, ya tafi shakatawa da karuwarsa inda ta tsinke masa mazakuta sakamakon rikici

Buhari, wanda ya sanar da jakadun manyan abubuwan da Najeriya za ta bai wa fifiko da kuma sabbin tsare-tsaren, ya kwatanta 'yan Najeriya da mutane masu matukar baiwa da kasar ta mallaka.

Ya ce daga cikin abubuwan da kasar za ta bai wa fifiko akwai farfado da tattalin arziki tare da habaka shi domin amfanin jajirtattun 'yan kasar.

Ya yi kira ga jakadun da su yi amfani da damar da suke da ita a kasar nan domin karfafa alakar da ke tsakanin gwamnatocinsu da mutanenta.

Buhari ya ce Najeriya za ta matukar dagewa wurin tabbatar da alaka mai karfi tsakaninta da kasashensu ba tare da wariya ba.

A wani labari na daban, domin kawo karshen rashin tsaro a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma, kamata yayi gwamnati ta fara tattaunawa da hukumomin tsaro, majalisar dinkin duniya ta sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin da ta gabata.

Dole ne a samu tattaunawa tare da siyasa don kawo maslaha da hanya mai bullewa ga hukumar soji, shugaban hukumar jin kai ta majalisar dinkin duniya da ke Najeriya, Edward Kallon yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel