UN ta sanar da Buhari hanya daya ta kawo karshen rashin tsaro

UN ta sanar da Buhari hanya daya ta kawo karshen rashin tsaro

Domin kawo karshen rashin tsaro a yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma, kamata yayi gwamnati ta fara tattaunawa da hukumomin tsaro, majalisar dinkin duniya ta sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin da ta gabata.

Dole ne a samu tattaunawa tare da siyasa don kawo maslaha da hanya mai bullewa ga hukumar soji, shugaban hukumar jin kai ta majalisar dinkin duniya da ke Najeriya, Edward Kallon yace.

Ya yi wannan zancen ne ga manema labaran gidan gwamnati a Abuja bayan taron da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kallon ya ce: "Rikicin na ci gaba kuma har yanzu ya ki tsagaitawa. Na sanar da shugaban kasa cewa, kari da kokarin dakarun sojin kasar nan, akwai bukatar a karfafa musu guiwa ta hanyar tattaunawa da su tare da yin amfani da salon siyasa wajen tabbatar da kawo karshen rikicin.

"A don haka ne muke tunanin ya kamata a yi amfani da salo daban-daban wurin shawo kan matsalolin.

"Amma idan kuka yi magana a kan rikici a Najeriya, muna magana ne a kan iri uku. Akwai wanda ake yi saboda kabilanci, wani saboda albarkatu sai wani kuma saboda mulki.

UN ta sanar da Buhari hanya daya ta kawo karshen rashin tsaro
UN ta sanar da Buhari hanya daya ta kawo karshen rashin tsaro. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dumu-dumu: An kama kwamandan Hisbah da laifin safarar kananan yara a Kano

"Dukkan kala ukun nan suna bukatar salo daban wurin shawo kansu. A yankin arewa maso yamma, ana fama da matsalar 'yan bindiga wacce babbar matsala ce. Akwai kuma ta kwadayin mulki.

"A don haka, saboda sarkewar dukkan rikice-rikicen nan uku a Najeriya, akwai wahalar kawo karshen shi da gaggawa saboda kowanne yana bukatar salo na daban ne.

"Amma kuma karkashin dukkan rikice-rikicen, akwai boyayyun abubuwa uku da yakamata a gano. Sune siyasa, tattalin arziki da kuma wayewar jama'ar. Suna da matukar amfani wurin kawo karshen matsalar.

“Alakar da ke tsakanin wadannan abubuwan uku na da matukar amfani idan aka duba ta'addanci, laifuka da kuma al'amuran 'yan bindiga.

"A don haka kira da nake ga shugaban kasa shine ya duba wadannan hanyoyin ta yadda zai iya shawo kan dukkan rikicin da ke addabar kasar nan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel