Masu caccakar Buhari basu kishin Najeriya - Gwamna Badaru

Masu caccakar Buhari basu kishin Najeriya - Gwamna Badaru

- Gwamnan jihar Jigawa, Gwamna Abubakar Badaru, ya kwatanta masu caccakar Buhari da masu gurbatacciyar zuciya da kuma rashin kishin kasa

- Ya tabbatar da cewa an samu manyan nasarori tare da ci gaba masu tarin yawa a Najeriya sakamakon mulkin shugaba Buhari

- Gwamnan ya kalubalanci jama'a da su duba nasarorin mulkin Buhari tare da alakanta shi da na gwamnatin da ta gabata

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar na jihar Jigawa, ya kwatanta masu kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari da masu gurbatacciyar zuciya da kuma rashin kishin kasa.

A yayin jawabi a taron mambobin APC na kafafen sada zumuntar zamani na yankin arewa maso yamma da aka yi a Dutse, gwamnan ya ce halin da tsaron kasar nan ke ciki ya gyaru.

Ba a hada yanzu da lokacin da ba, da mayakan ta'addanci na Boko Haram ke kai wa jama'a hari a wuraren bauta, kasuwanni, tashoshin mota da sauran wurare, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Badaru ya kara da cewa, a yanayin ayyukan inganta rayuwa da gwamnatin Buhari ta yi, za a iya cewa ya cika alkawurran da ya daukarwa 'yan Najeriya.

Ya kalubanci 'yan Najeriya da su fito su duba nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu, sannan a alakanta su da na gwamnatin da ta gabata.

Masu caccakar Buhari basu kishin Najeriya - Gwamna Badaru
Masu caccakar Buhari basu kishin Najeriya - Gwamna Badaru. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda jirginmu ya kusa ragargajewa a sararin samaniya - Aisha Buhari

A wani labari na daban, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta nuna yakinin yin nasara a zaben gwamnoni mai zuwa a jihohin Edo da Ondo.

Jam’iyyar mai mulki ta sanar da wannan tabbaci ne bayan kaddamar da kwamitin sasanci nata a jihohin Imo da Ogun a ranar Juma’a, 21 ga watan Agusta, a Abuja, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana kan ci gaban, Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana cewa bayan sasancin, su kansu fusatattun mambobi za su dawo jam’iyyar sannan su taimaka wajen karfafata gabannin zaben 2023.

Gwamna Buni ya bayyana cewa APC za ta shayar da fannin siyasar Najeriya mamaki da dawowar manyan tsoffin jiga-jiganta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel