Hotunan dan majalisa Alhassan Ado-Doguwa da matansa 4 tare da 'ya'ya 27

Hotunan dan majalisa Alhassan Ado-Doguwa da matansa 4 tare da 'ya'ya 27

- Wasu kyawawan hotun shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, Alhaji Alhassan Ado-Doguwa tare da iyalinsa sun bayyana

- A hoton mai matukar kayatawar, an ga dan majalisar zaune cikin matansa hudu tare da 'ya'ya maza da mata har 27

- A watan Janairun da ya gabata, Doguwa ya je karbar rantsuwa a majalisar wakilan tare da matansa hudu cas inda ya bayyana cewa 'ya'yansa 27

Shugaban masu rinjaye, Alhassan Ado-Doguwa, ya bayyana a cikin matansa hudu da yaransa 27, lamari mai bada sha'awa da birgewa.

A watan Janairun wannan shekarar ne Ado-Doguwa ya bayyana cewa yana da mata hudu da 'ya'ya 27.

Ya sanar da hakan ne a lokacin da za a rantsar da shi a majalisar wakilan.

Ya sanar da manema labaran majalisar cewa, mahaifinsa ya rasu yana da shekaru 86 kuma ya bar 'ya'ya 40 rayayyu, a ciki har da mai shekaru hudu a duniya.

Hotunan dan majalisa Alhassan Ado-Doguwa da matansa 4 tare da 'ya'ya 27
Hotunan dan majalisa Alhassan Ado-Doguwa da matansa 4 tare da 'ya'ya 27. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsohon gwamna a Najeriya ya yi kaca-kaca da karuwarsa, 'yan sanda sun damkesu

Hotunan dan majalisa Alhassan Ado-Doguwa da matansa 4 tare da 'ya'ya 27
Hotunan dan majalisa Alhassan Ado-Doguwa da matansa 4 tare da 'ya'ya 27. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

Idan za mu tuna, Dan majalisan wakilan tarayya mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa 'yaya 27 matansa hudu suka haifa masa kuma zasu cigaba da hayayyafa.

Yayin da ake zaman majalisar ranar wata Laraba, Doguwa ya gabatar da matansa hudu gaban yan majalisar.

Yayin da ake rantsar da shi matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar, ya bayyana cewa ya kawo matansu hudu domin yan majalisar su gansu.

"Kakakin majalisa, ina mai farin cikin fada muku cewa mata na hudu na tare da ni a nan yau," Doguwa ya labarta, kafin umartar matan su mike tsaye gaban yan majalisa.

"Ya mai girma kakakin majalisa, wadannan mata nawa hudu da kuke gani sun haifa mini 'yaya 27, kuma muna cigaba," ya jaddada.

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC ta alanta Alhassan Ado Doguwa, matsayin zakaran zaben mai-mai, mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa a majalisar wakilan tarayya.

Baturen zaben, Farfesa Mansur Bindawa, ya bayyana cewa Ado Doguwa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya samu kuri'u 66,667 yayinda abokin hamayyarsa Yusha’u Salisu na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP ya samu kuri'u 6,323.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel