Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun yi awon gaba da yaya da ƙanwa a Katsina

Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun yi awon gaba da yaya da ƙanwa a Katsina

Yan bindiga sun harbe wani Nasiru Aliyu mai shekaru 37 har lahira a garin Gidangizo da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Mazauna garin sun ce ƴ a bindigan sun kuma raunatta mutane hudu kuma suka yi awon gaba da wasu mata biyu ƴaya da ƙanwa; Amina Mudi, 23 da Zainaru, 20.

Rahotonni sun ce ƴan bindigan sun isa garin Gidangizo ne a kan babura misalin ƙarfe 12.30 na dare suka rika bi gida-gida suna neman abinci da kuɗi.

Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun yi awon gaba da yaya da ƙanwa a Katsina
Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun yi awon gaba da yaya da ƙanwa a Katsina
Asali: UGC

An kashe Aliyu ne yayin da ƴan bindigan suka shiga gidansa suka nemi ya basu kuɗi amma ya ce ba shi da kuɗi.

DUBA WANNAN: A shirye na ke in ba da rayuwata kamar Mandela, inji Mailafia bayan DSS ta sako shi

The Punch ta ruwaito cewa harbi suka yi masa na kusa ta yadda zai yi wahala ya sha.

Mazauna garin sun kuma ce yan bindigan sun yi kutse gidan wani Alhaji Mudi inda suka yi awon gaba da ƴan uwansa biyu; Amina da Zainaru.

Ɗaya daga cikin mazauna garin ya ce, "Ƴan bindigan sun ɗara 12 kuma dukkansu da bindigunsu. A kan babura suka zo; sun kashe Aliyu saboda ya yi jayayya da su cewa ba shi da kuɗi a lokacin da suka nemi ya basu kuɗi.

"Sun masa harbi na kusa. Ƴan bindigan gida-gida suka rika bi. A gidan Alhaji Mudi, sun yi awon gaba da ƴaƴansa mata biyu. Yan bindigan sun raunata mutane da dama."

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Kazalika, wasu rahotanni da ba a tabbatar da sahihancinsu ba sun ce an sace wani maaikacin laffiya da ke aiki a daya daga cikin asibitin gwamnati a Nahiyar da ke karamar hukumar Dandume.

An sace likitan haƙorin da yanzu ba a tabbatar da sunansa ba a daren Talata yayin da ƴan bindiga suka kai hari garinsu kuma har zuwa Laraba ba a san inda ya ke ba.

Kakakin ƴan sandan ya ce a bashi lokaci ya yi bincike a kan labarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel