Batan ga Annabi: Kotun Kano ta zartar da hukuncin kisa ga matashin mawaki

Batan ga Annabi: Kotun Kano ta zartar da hukuncin kisa ga matashin mawaki

- Babbar kotun shari'a da ke zamanta a Kano ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan matashin da aka gurfanar da laifin batanci ga annabi Muhammad

- Wasu fusatattun matasa sun rushe gidan su matashin mawakin bayan ya wallafa wata waka a cikin watan Maris

- A wani hukunci da kotun ta zartar, wani matsi zai shafe shekaeru 10 a gidan bayan samunsa da lafin yin furucin raini a an Allah

Wata babbar kotun Shari'a da ke zamanta a Hausawa Filin Hockey da ke cikin birnin Kano ta zartar da hukuncin kisa a kan wani matashi mai shekaru 22 saboda wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga Annabi Muhammad.

Daily Ngerian ta wallafa cewar wata jaridar yanar gizo mai suna 'Focus' da ke Kano ta bayyana cewa alkalin kotun, Khadi Aliyu Muhammad, ya zartar da hukuci a kan matashin, Yahaya Aminu Sharif, a yau, Litinin.

Jaridar ta bayyana cewa Khadi Muhammad ya zartar da wannan hukunci ne bayan ya gamsu da hujjojin cewa matashin ya aikata laifin da ya jawo aka gurfanar da shi a gaban kotun.

Batan ga Annabi: Kotun Kano ta zartar da hukuncin kisa ga matashin mawaki
Kotun Kano ta zartar da hukuncin kisa ga matashin mawaki
Asali: Twitter

An gurfanar da matashin mawaki Yahaya a gaban kotu bayan an zargeshi da wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga annabi Muhammad a cikin watan Maris na shekarar 2020.

DUBA WANNAN: Direbobin tankar man fetur sun shiga yajin aiki

Bayan wallafa wakar da kuma yaduwarta a dandalin sada zumunta, musamman Whatsapp, wasu fusatattun matasa sun kone gidan su matashin tare da jagorantar zangaz-zanga zuwa hedikwatar hukumar Hisbah.

A cewar rahoton jaridar 'Focus' da Daily Nigerian ta kara yadawa, kotun ta zartar da hukuncin daurin shekaru 10 a kan wani matashi mai suna Umar Farouq sakamakon furta kalaman raini a kan Allah.

An gurfanar da Farouq a gaban kotun ne bisa tuhumarsa da furta kalaman raini ga Allah yayin musu da abokansa a unguwar Sharada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel