Tarbiya tayi wahala, 'yan damfarar yanar gizo sun zama madubin dubawa - Diezani

Tarbiya tayi wahala, 'yan damfarar yanar gizo sun zama madubin dubawa - Diezani

- Tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke, ta koka kan tabarbarewar tarbiya a tsakanin jama'a

- Diezani ta ce a wannan zamani, 'yan damfarar yanar gizo sun zama madubin dubawa cikin mutane

- Tsohuwar ministar dai ta koma zama kasar Landon bayan saukar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan daga mulkin Najeriya a 2015

Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur, ta jajanta yadda tarbiya ke barin jama'a.

A yayin jawabi a taron yanar gizo na kungiyar cigaban Ijaw, tsohuwar ministar ta ce al'amuran sun lalace ta yadda 'yan damfarar yanar gizo suka zama abun mutuntawa a al'umma.

Ta bayyana amfanin zama jagora ga matasa don aiki tukuru ne ke kawo nasara.

"Yan damfarar yanar gizo masu salon zamani a yanzu sune madubin dubawa. Wadannan sune ke koyar da miyagun dabi'u ga al'umma," tace.

"Wannan abun takaici ne da ya samesu. Dalilin mene yasa nake daukar lokaci wurin magana a kan gidajen marayu da amfanin su ga yaranmu? A gaskiya duk yaro wanda ba nagari ba, shine yake girma ya zama magidancin banza kuma haka rayuwar ke ci gaba. Ba za ka shuka masara ba kace shinkafa kake so ba."

Tarbiya tayi wahala, 'yan damfarar yanar gizo sun zama madubin dubawa - Diezani
Tarbiya tayi wahala, 'yan damfarar yanar gizo sun zama madubin dubawa - Diezani Hoto: Daily Post
Asali: Twitter

Jackson Use, mawallafin Point Blank News ne ya saki bidiyon jawabin Diezani a taron.

Tsohuwar ministar ta koma zama kasar Landon bayan saukar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan daga mulkin Najeriya a 2015.

KU KARANTA KUMA: Jerin 'yan siyasa 4 da Obasanjo ya disashesu a Najeriya

A wannan shekarar, an fara tuhumar Alison-Madueke a wata ofishin 'yan sanda da ke Landon.

Ana zargin tsohuwar ministan ne da laifin cin hanci da kuma watanda da wasu kudade, lamarin da yasa aka damketa.

Ministan ta gurfanar a gaban wata kotun majistare inda daga bisani aka bada belinta amma aka kwace fasfotinta.

Kotun ta kwace £27,000 daga wurin ta yayin da cibiyar ta bukaci a tsare Beatrice Agama, mahaifiyarta da Melanie Spencer tare sa Alison-Madueke.

A yayin bincikar ta da ake yi a Ingila, hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta duba gidanta da ke Asokoro, a Abuja.

Amma har yanzu ba a ji komai ba a kan lamarin bayan shekaru uku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel