Ba zan yi takarar shugaban kasa ba a 2023, Kudu na ke son su karbi mulki - El-Rufai

Ba zan yi takarar shugaban kasa ba a 2023, Kudu na ke son su karbi mulki - El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa ba zai yi takarar shugabancin kasa ba zaben shekarar 2023.

Gwamnan ya ce yana son a bawa yankin kudancin Najeriya damar su fitar da shugaban kasa a shekarar 2023 bayan wa'adin shugaba Muhammadu Buhari ta kare a wata zantawa da BBC Hausa ta yi da shi.

Ba zan yi takarar shugaban kasa ba a 2023, Kudu na ke son su karbi mulki - El-Rufai
Ba zan yi takarar shugaban kasa ba a 2023, Kudu na ke son su karbi mulki - El-Rufai
Asali: Facebook

Ya ce: "Mutane da dama sun dade suna cewa ina son yin takarar shugaban kasa tun lokacin da na ke ministan babban birnin tarayya, Abuja.

"Banga wata hikima a hakan ba.

"Bana shaawar yin takarar shugabancin Najeriya.

"Allah ne ke bada mulki, ko kana so ko ba ka so.

"Idan Allah yana so, zai baka mulki, amma ni ban taba saka wa a rai ne cewa zan yi takarar shugabancin Najeriya ba kuma babu wanda zai taba cewa na fada hakan," in ji shi.

El Rufai ya ce akwai yarjejeniya cewa idan arewa ta yi mulki na shekaru takwas, za a bawa kudancin kasar mulkin kuma yan siyasa sun san da batun duk da cewa ba ya cikin kundin tsarin mulki.

DUBA WANNAN: Matar Ahmed Musa ta haifi ɗa namiji

Gwamnan da ke kan waadinsa na biyu ya ce: "Wannan ne yasa na fito na ce kada wani dan arewa ya fito neman takarar shugaban kasa bayan waadin Shugaba Buhari ta kare.

"A bari 'yan kudancin Najeriya suyi mulkin na shekaru takwas".

A bangarensa, dan uwan Shugaba Buhari, Mallam Mamman Daura a ranar Talata 27 ga watan Yuli ya ce babu bukatar a rika karba karba wurin zaben shugaban kasar Najeriya.

Daura ya ce cancanta yafi dacewa a duba wurin tsayar da dan takarar shugaban kasar a 2023.

Manyan jamiyyun siyasar kasar PDP da APC da wasu kungiyoyi a kasar sun nuna kin amincewarsu da abinda Daura ya fadi game da zaben shugaban kasar.

Fadar shugaban kasa ita ma ta nisanta kanta da batun inda ta ce abinda ya fadi raayinsa ne kawai ba matsayar fadar gwamnati ba.

Duk da yana son a bawa kudancin Najeriya damar tsayar da shugaban kasa, El Rufai ya ce a duba cancanta.

El Rufai shi a kullum cancanta ya ke duba wa ba bangaranci ba wurin nada mukamai.

"Idan ka duba yadda na ke tafiyar da mulki na, bana laakari da bangaren da mutum ya fito.

"Cacanta da kwazon aiki da yi wa alumma hidima na ke duba wa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel