Badakalar NDDC: Akpabio ya saki sabbin sunaye, ya ambaci tsoffin gwamnoni 3 da suka samu kwangiloli

Badakalar NDDC: Akpabio ya saki sabbin sunaye, ya ambaci tsoffin gwamnoni 3 da suka samu kwangiloli

Rahotanni sun kawo cewa ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio ya alakanta wasu tsoffin gwamnoni uku da wasu ayyukan kwangiloli da hukumar ci gaban Neja Delta (NDD) ta bayar.

A cewar jaridar The Sun, Akpabio ya yi zargin cewa gwamnoni biyu daga jihar Delta sun aiwatar da wasu kwangilolin hukumar.

An kuma tattaro cewa ministan ya ambaci sunan tsohon gwamnan Abia a matsayin wanda ya amfana daga kwangilolin.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya basu fahimci ra'ayin Mamman Daura ba kan tsarin shugabanci - Tsohon Gwamna

Badakalar NDDC: Akpabio ya saki sabbin sunaye, ya ambaci tsoffin gwamnoni 3 da suka samu kwangiloli
Badakalar NDDC: Akpabio ya saki sabbin sunaye, ya ambaci tsoffin gwamnoni 3 da suka samu kwangiloli Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Jaridar ta bayyana cewa sunayen da Akpabio ya ambata a cikin jawabin sun hada da:

1. Emmanuel Uduaghan (tsohon gwamnan jihar Delta)

2. James Ibori (tsohon gwamnan jihar Delta)

3. Sanata Uzor Kalu (tsohon gwamnan jihar Abia)

4. Sanata Ifeanyi Ararume

Sai dai kuma a martaninsa Uzor Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia wanda ya ke a matsayin bulaliyar majalisar dattawa a yanzu ya ce hukumar NDDC bata biya ‘yan kwangilar da suka gina hanyoyin da ya gudanar ba.

Kalu a wani jawabi dauke da sa hannun Barista Emeka Nwala ya ce maganar da ke kasa a yanzu a hakumar NDDC shine batu batar kudade ba wai na ayyukan da aka yi ba.

Ya yi bayanin cewa ayyukan hanyar da ministan ya ambata sun kasance na shiga tsakani da shi ya yi domin al’umma a lokacin yana mai zaman kansa kafin zama sanata.

KU KARANTA KUMA: Babu wani mutum da nake tsaro sai Allah – Gwamna Obaseki

Ya ce an ambaci sunansa ne saboda ya yi amfani da takarda mai dauke da sunansa wajen rubuta wasikar tausayawa zuwa ga hukumar NDDC a 2016, inda ya roki hukumar da ta ceto hanyoyi a Abia.

“NDDC a yayinda suka duba hakan wanda na gode ma hakan, sun bayar da ayyukan hanyoyi ga kamfanonin da suka nemi kwangiloli amma ba wai ni suka baiwa ba. Nasabar da ke tsakanina da aikin shine saboda an aiwatar da ita ne sakamakon shiga tsakani da na yi,” in ji Kalu.

A baya mun ji cewa Majalisar Wakilai ta yi barazanar yin karar Akpabio a kotu kan ikirarin da ya yi na cewa kaso mai yawa cikin kwangilolin NDDC, yan majalisan ne aka bawa.

Ministan ya yi wannan ikirarin ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar da aka kafa domin duba kudaden da ake kashewa a hukumar da ake ganin ya wuce hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel