Shugaban BUK mai barin gado, Farfesa M. Y. Bello, ya samu mukami a gwamnatin Ganduje

Shugaban BUK mai barin gado, Farfesa M. Y. Bello, ya samu mukami a gwamnatin Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nada shugaban jami'ar BUK mai barin gado, Farfesa Mohammed Yahuza Bello, matsayin shugaban gudanarwa na jami'ar Yusuf Maitama mallakar jihar Kano (YUMSUK).

Da ya ke sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, kwamishinan yada labaran jihar Kano; Malam Muhammad Garba, ya ce nadin Farfesa Yahuza ya fara aiki nan take.

Zangon mulkin Farfesa Yahuza a matsayin shugaban jami'ar BUK zai kare a karshen watan Agusta.

An zabi Yahuza, Farfesan lissafi, a matsayin shugaban jami'ar BUK a shekarar 2015.

Farfesa Yahuza ya taba rike mukamin shugaban ilimin kimiyyar lissafi a jami'ar BUK daga shekarar 1991 zuwa 1999 da shugaban tsangayar ilimin kimiyya daga shekarar 1995 zuwa 1999.

Sauran mukaman da ya rike kafin ya zama shugaban jami'ar BUK sun hada da rike kujerar darektan cibiyar sadarwa (ICT) daga shekarar 2002 zuwa 2007, shugaban tsangayar karatun gaba da digiri da kuma rike kujerar mataimakin shugaban BUK.

Shugaban BUK mai barin gado, Farfesa M. Y. Bello, ya samu mukami a gwamnatin Ganduje
Ganduje da Farfesa M. Y. Bello
Asali: Facebook

A ranar 12 ga watan Yuni ne tsohon shugaban gudanarwa na jami'ar YUMSUK, Sule Yahaya Hamma, ya yi murabus daga mukaminsa.

DUBA WANNAN: Karamin soja ya budewa babban soja wuta a jihar Borno

Domin nuna jin dadin irin gudunmawar da ya bayar, gwamna Ganduje ya sauya sunan wani bangare na sabon titin zuwa Maiduguri zuwa sunan Sule Yahaya Hamma.

Hamma dattijo ne da ya rike mukamai daban - daban a gwamnatin jihar Kano kafin ya yi murabus a matsayin sakataren gwamnatin jihar Kano daga 1979 zuwa 1983.

An bashi lambar karramawa ta gwamnatin tarayyar Najeriya (MFR) a shekarar 1983.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel