Kyawawan hotunan 'ya'ya mata na Bashir El-Rufai, dan uwan gwamnan Kaduna
Kyawawan hotunan 'ya'ya mata na Bashir El-Rufai, dan uwan gwamnan jihar Kaduna, sun kawata kafafen sada zumuntar zamani a ranar Idin babbar sallah.
A hotunan da suka saki da yammacin ranar Alhamis ta shafin Twitter na Munah El-Rufai, daya daga cikin 'yan mata, an ga kyawawan 'yan mata sanye da wanduna da riguna iri daya.
A hotunan da 'yan matan suka matukar kawatarwa, sun saka dogayen wanduna masu kalar bula tare da riguna masu dogayen hannu kalar kasa.
Tun bayan da hotunan suka bazu a shafukan sada zumunta, mutane da yawa ballantana samari, sun hanzarta yin tsokaci a kan kyawunsu.
Wasu kuwa nunawa suke a yau Allah ya hada su da matan da suke dade suna mafarkin mallaka.
Ga kyawawan hotunan 'yan matan.

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng