‘Yan Bindiga Sun Sake Auka wa Kaduna, Sun Kuma Yin Garkuwa da Bayin Allah

‘Yan Bindiga Sun Sake Auka wa Kaduna, Sun Kuma Yin Garkuwa da Bayin Allah

  • ’Yan bindiga sun koma Millennium City, Kaduna, inda suka yi garkuwa da mutane takwas a tashin farko
  • Ana cewa wai sojoji sun bi sawun maharan, har aka ceto wasu daga cikin waɗanda aka nemi a dauke
  • Iyalan waɗanda aka sace sun roƙi gwamnati da jami’an tsaro a gaggauta ceto sauran mutanen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kaduna - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari a Kaduna kuma sun sake yin gaba da jama’a.

An shiga rukunin gidajen Nuru Suraj Estate da ke yankin Millennium City, a cikin birnin Kaduna an dauke mutum shida.

Uba Sani
Gwamnan Kaduna, Uba Sani tare da iyalin Ahmad Zakka da wani jami'in tsaro a kauyen Kajuru Hoto: Uba Sani/Getty Images
Source: UGC

'Yan bindiga sun kuma dauke mutane a Kaduna

Rahoton da aka samu daga Daily Trust ya ce cikin mutanen da aka yi gaba da su, har da ɗaliban makarantar sakandare.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga wannan unguwa da aka matsa mata ne a cikin tsakar dare a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Ana jimamin Masussuka, 'yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun yi ta'addanci

Sun kutsa gidaje biyu da ke maƙwabtaka da juna, a nan suka yi awon gaba da mutane takwas kafin su saki wasu matum biyu.

An kyale wadanan biyun ne ganin cewa tsofaffi ne, ganin yawan shekarunsu. Wani kaulin kuma ya ce sojoji suka cece su.

Mazauna Millenium City na cikin dar-dar

Wata mazauniyar yankin, Mamar Hamid ta ce maharan sun samu damar kutsowa unguwarsu ne wata ƙofar shiga ta biyu.

Matar ta ƙara da cewa lamarin ya jefa mazauna yankin Millenium City a cikin firgici.

An ce sojoji sun bi sawun maharan har aka samu nasarar ceto wasu daga cikin waɗanda aka sace, amma miyagun sun tsere.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, mutum akalla shida na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutanen.

Yadda aka sace ɗalibai 2 cikin daren

Abdullahi Wada, wanda jikokinsa biyu ke cikin waɗanda aka sace, ya tabbatar da faruwar lamarin ga ‘yan jarida ranar Talata.

Maharan sun fara shiga gidan ’yar Alhaji Wada, suka yi garkuwa da yaran wato jikokinsa biyu.

Ya bayyana cewa yaran, masu shekaru 14 da 13, suna ajin sakandare na biyu (JSS 2) da na farko (JSS 1), a garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Lauya ya ga hannun Tinubu wajen neman hana Pantami da Aminu Gwarzo shiga takara

Maharan sun yi gaba da mutum 4 a gida

A cewarsa, bayan sun sace yaran, maharan sun shiga gidan maƙwabta, suka sace wani mutum, matarsa da ’ya’yansu biyu.

Wada ya ce maharan sun saki wasu mata biyu tsofaffi da suka sace saboda tsufansu.

Ya yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa domin tabbatar da kuɓutar da mutanen da har yanzu suke hannun miyagun.

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Abbas ya ce shi da matarsa suna kallon talabijin a ɗakinsu suka ji ƙarar harbe-harbe.

Ya ce nan take suka kashe talabijin, sannan ya yi ƙoƙarin kiran wani abokinsa amma bai samu damar ankarar da shi a lokacin ba.

Jaridar Leadership ta ce babu wata sanarwa da ta fito daga bakin hukuma ko jami’an tsaro tun lokacin da abin ya faru har yanzu.

Sai dai wani babban jami’in tsaro da ba a ba shi izinin yin magana da manema labarai ba ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya.

Kara karanta wannan

Rashin imani: An ɗaure mutum 3 da ake zargi da sace ƙaramin yaro kuma suka kashe shi a Kano

Rahotanni sun nuna Kwamishinan ’Yan Sandan jihar Kaduna, Muhammad Rabiu ya ziyarci yankin domin duba halin da ake ciki.

'Yan sanda
'Yan sanda a Kaduna lokacin zabe Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Lokacin da 'yan bindiga suka sace Zakkah

An ji labarin yadda Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan sace Ahmed Zakka, matarsa da jaririyarsu mai watanni shida a Kaduna.

Masu garkuwa da mutanen sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 300, tare da barazanar kashe Zakka idan ba a biya miliyoyin ba.

Atiku da ɗan majalisarsa, Bello El-Rufai sun buƙaci jami’an tsaro su gaggauta ceto su kuma a karshe an yi nasara wajen yin hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng