Tsaka mai wuya: Hukumar CCB ta na shirin gurfanar da Magu

Tsaka mai wuya: Hukumar CCB ta na shirin gurfanar da Magu

Hukumar da'ar ma'aikata (CCB) ta shirya tuhumar Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), bisa zarginsa da kin bayyana kadarorinsa, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

Wannan sabuwar tuhumar daban ta ke da tuhumar da kwamitin bincike da shugaban kasa ya kafa ke yi wa Magu.

Wata majiyar jaridar TheCable ta bayyana cewa CCB za ta gurfanar da Magu a gaban kotun da'ar ma'aikata (CCT) kamar yadda ta saba gurfanar da jami'an gwamnati da su ka ki bayyana kadarorinsu.

Sai dai, Lauyan Magu ya musanta cewa wanda ya ke karewa bai bayyana dukiyarsa ba.

A ranar Litinin ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa Magu ya ce a shirye ya ke ya fara amfani da kafafen sadarwa domin kare kansa daga dukkan tuhume - tuhumen da ake yi masa.

Magu ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da lauyansa, Wahab Shittu, ya fitar ranar Lahadi, inda ya ke musanta cewa an yi almundahana da kudaden da EFCC ta kwace daga hannun NNPC a lokacin Magu.

Shittu ya bayyana cewa kwamitin bincike da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa bashi da masaniya a kan wasu zarge - zargen badakala da ake alakantasu da Magu.

Tsaka mai wuya: Hukumar CCB ta na shirin gurfanar da Magu
Ibrahim Magu
Asali: UGC

Lauyan ya bayyana cewa EFCC ta saka kudin da ta kwato a asusun NNPC bisa wani tsari da hukumomin biyu mallakar gwamnati da wasu manyan dillalan man fetur suka amince da shi, kuma an saka kudin ta asusun bai daya na kasa (TSA).

A cewar lauyan, duk wani mai shakku a kan hakan zai iya tabbatar da gaskiyar maganar ta hanyar tuntubar hukumar NNPC ko kuma ya ziyarci sashen adana bayanai na hukumar EFCC.

DUBA WANNAN: N-Power: 'Yan Najeriya sun yi gangami zuwa fadar Aso Villa

Shittu ya bayyana mamakinsa a kan yadda aka ko kadan maganar mayarwa da NNPC kudin bata kai gaban kwamitin binciken ba.

Sauran zarge - zargen da Shittu ya kare sun hada da batun zargin Magu da kin bayyana kadarorinsa kamar yadda doka ta bukata da kuma tsame wasu mutane daga tuhumar badakalar biliyan uku a hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS).

Ya kara da cewa an kitsa zarge-zargen ne kawai da gan-gan domin a kunatatawa Magu sannan a bata sunansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel