Bene hawa biyu ya rushe a Abuja, ya ritsa da mutum 10

Bene hawa biyu ya rushe a Abuja, ya ritsa da mutum 10

Wani bene mai hawa biyu da ake ginawa a Abuja ya rushe tare da ritsawa da mutane 10 da kuma yi wa wani mutum guda mummunan rauni.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a bayan kasuwar zamani da ke unguwar Dawaki a yankin Galadima a birnin tarayya, Abuja.

Lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 10:40 na safe, ya yi sanadiyyar raunata leburorin da ke aiki, wadanda kuma sune mazauna benen..

Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da takwarorinsu na birnin tarayya (FEMA) sun gaggauta zuwa wurin tare da tserar da mutanen bayan an sanar dasu.

An garzaya da mutum guda da ya samu mummunan rauni tare da wasu mutane biyu zuwa asibiti mafi kusa.

Idris Abbas, babban darektan FEMA, ya ce basu bata lokaci ba wajen aika jami'ansu bayan samun labarin rushewar benen ta hanyar kiran lambobin wayarsu na 'ko ta kwana'.

Bene hawa biyu ya rushe a Abuja, ya ritsa da mutum 10
Bene hawa biyu ya rushe a Abuja
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa tun asali akwai gini a wurin, amma sai mai wurin ya yanke shawarar mayar da shi bene.

DUBA WANNAN: Ambaliyar ruwan sama ta yi 'tafiyar yaji' da mutane 30 a Abuja

"Lamarin ya ritsa da mutane 10, an kubutar da mutane uku sannan an garzaya dasu zuwa asibiti," a cewarsa.

Kazalika, ya gargadi masu gidaje da kangwaye su guji saba ka'idar yin gine - gine wacce hukumar raya birnin Abuja ta tsara.

Abbas ya kara da cewa hukuma ta dakatar da maigidan daga aikin dora bene a kan tsohon gidansa amma ya yi kunnen kashi, ya zabi a yi masa aiki yayi hutun karshen mako.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel