Bincike: Hoton yaron da ke shan gurbataccen ruwa ba daga Neja Delta yake ba

Bincike: Hoton yaron da ke shan gurbataccen ruwa ba daga Neja Delta yake ba

Wani shafi a kafar sada zumuntar zamani mai suna Indigenous People of Niger Delta mai mabiya 42,158, ya wallafa hoton wani yaro yana shan gurbataccen ruwa daga rafi.

Shafin ya yi ikirarin cewa anyi hoton a ranar 9 ga watan Yulin 2019, kuma cewa nan ne wurin da jama'ar masarautar Egbema suke samun ruwan amfani duk da kuwa gurbacewar da ruwan yayi da man fetur da iskar gas a yankin Neja Delta.

Hakazalika, wani shafi mai suna SweerGlobal ya wallafa hoton inda ya rubuta a kasansa cewa yaro ne daga jihar Bayelsa yake shan ruwa.

KU KARANTA KUMA: Kaduna: 'Yan sanda sun yi babban kamu, sun kama 'yan bindiga 217

Bincike: Hoton yaron da ke shan gurbataccen ruwa ba daga Neja Delta yake ba
Bincike: Hoton yaron da ke shan gurbataccen ruwa ba daga Neja Delta yake ba Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shafin ya kara ikirarin cewa, "mazauna yankin Neja Delta miliyan 30 ne ke shan ruwan rafin."

Shafin ya yi ikirarin cewa hoton an dauke shi ne daga masarautar Egbema da kuma jihar Beyelsa da ke yankin Neja Delta ta Najeriya.

Sai dai bincike da jaridar Daily Trust ta ruwaito ya tabbatar da cewa babu gaskiya a lamarin.

KU KARANTA KUMA: Ma'aikatar kwadago ga majalisar: Keyamo ne zai kula da daukar aiki 774,000

Gurbataccen ruwan ba shi bane inda jama'ar masarautar Egbema ke samun ruwa ba. Babu kuma kamshin gaskiya da aka ce jama'a miliyan 30 ke amfani da irin wannan ruwan.

An gano cewa an dauka hoton ne a Akpatoeme da ke Ketu ta arewa na kasar Ghana.

A wani labari na daban, gwamnatin Jihar Niger a ranar Laraba ta sanar da cewa almajiri 64 da suka kamu da korona a jihar sun warke, an kuma mayar da su gidajensu don sada su da iyalansu.

Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Asibiti, Dr. Mohammed Makusidi ya sanar da hakan yayin da ya ke amsa tambayoyin ƴan jarida a Minna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce, "Kamar yadda muka fadi a baya, muna da mutum 166 da suka kamu da Covid-19 cikinsu har da almajirai.

"An yi wa almajirai 1075 gwajin coronavirus cikinsu 64 suna dauke da kwayar cutar.

"Sai dai abin farin ciki yanzu dukkansu 64 sun warke kuma an sada su da iyalansu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel